Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace sabuwar kujerar Kawu Sumaila

Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace sabuwar kujerar Kawu Sumaila

Babban kotun tarayya dake zaune a Kano a ranar alhamis ta kwace kujerar tsohon hadimin Buhari, Kawu Sumaila, na zababben dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Sumaila/Takai na jihar Kano.

Sumaila, wanda ya kasance hadimin shugaba Buhari kan majalisar wakilai, ya lashe zaben kujerar karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kotun ta umurci hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta tabbatar da Shamsuddeen Dambazzau matsayin wanda ya lashe zabe.

Dambazau, wanda haifaffen dan ministan harkokin cikin gida, Janar Abdurrahman Dambazau, ne ya shigar da Kawu Sumaila da APC kotu rashin adalcin da yake ganin an yi masa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata - Majiya

Dambazau ya bayyanawa kotu ta bakin lauyansa, Nuraini Jimoh, cewa Kawu Sumaila takarar kujerar sanata ta kudu yayi kuma ya sha kasa hannun Kabiru Gaya.

Hakikani gaskiya shine Kawu Sumaila bai yi musharaka a zaben kujerar ba amma jam'iyyar ta bashi tikitin saboda kwantar da kura tsakanin 'yayan jam'iyya bayan ya fadi a zabe.

Alkalin ya yanke cewa abinda APC tayi ya sabawa doka saboda Sumaila bai musharaka a zaben fidda gwani ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel