Rikicin Zamfara: Ana zargin mataimakain shugaban karamar hukumar Anka da alaka yan bindiga, an damke shi

Rikicin Zamfara: Ana zargin mataimakain shugaban karamar hukumar Anka da alaka yan bindiga, an damke shi

-Jami'an soji sun damke mataimakin shugaban karamar hukumar Anka

-Wasu mutum biyu su ma sun shiga hannun jami'an soji a jihar Sakkwato

Jami’an dake karkashin rundunar mayakan ‘Operation Sharan Daji’ ne suka samu nasarar cafke mataimakin shugaban karamar hukumar Anka, Yahuza Wuya wanda ake zarginshi da cewa yanada alaka da yan ta’adda.

Mukaddashin jami’i mai kula da yada labarai na mayakan, Manjo Clement Abiade ya tabbatar da kama Yahuza Wuya yayinda yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis. Yace an kama mataimakin shugaban karamar hukumar ne ranar 13 ga watan Afrilu, a bisa ga wasu bayanai na sirri da muka samu cewa yana da alaka da kungiyar yan ta’addan dake addabar kauyukan Wuya da Sunke.

Rikicin Zamfara: Jami’an soji sun kama mataimakain shugaban karamar hukumar Anka

Operation Sharan Daji
Source: Twitter

KU KARANTA:Majalisar wakilai ta mika kudurin neman a bude kwalejin fasaha da kere-kere mallakar Gwamnatin tarayya a Fagge

Ya kara da cewa, “Yahuza ya kasance yana taimakama yan ta’addan wajen siyar da shanun da suke sace da kuma jakai, kana kuma yana sanar dasu duk wani motsi da rundunar sojin keyi tare da ma wasu kungiyoyin tsaro ciki har da yan sintiri.”

Bugu da kari, jami’in ya sake shaidawa yan jarida cewa “shi wannan mutum shine wanda yayi ruwa yayi tsaki aka fidda wani hatsabibin dan bindiga mai suna Sani Yaro daga gidan yarin Gusau.”

A wani labarin mai kama da wannan, Abiade ya bada tabbacin cewa mayakan sun samu nasarar kama mutane biyu wadanda ake zargin cewa yan leken asirin yan ta’addan ne, a tsakanin titin Burukusuma zuwa Sabon Birni dake jihar Sakkwato. In da ya bayyana sunayensu a matsayin; Mallam Ibrahim Bangaje da kuma Mallam Ado Bayero.

Ba tare da bata lokaci ba, zamu mika su zuwa ga jami’an tsaro da suka dace domin a tuhumesu kana kuma ayi musu hukuncin da yayi daidai da laifukansu.

Shi kuwa babban Kwamandan mayakan Operation Sharan Daji, Janar Hakeem Otiki ya kara jinjinama mayakan akan fadi tashin da suke na ganin cewa jihohin, Zamfara, Kebbi, Katsina da Sakkwato sun samu zaman lafiya mai dorewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel