Kakakin majalisa: Kungiyar matasa sunce lallai Wase ne zabinsu

Kakakin majalisa: Kungiyar matasa sunce lallai Wase ne zabinsu

Kungiyar matasan Najeriya masu kare damokradiyya (CNYDD) sunce lallai mataimakin Shugaban masu rinjaye a malisar wakilai, Hon. Ahmed Idris Wase suke so a matsayin kakakin majalisar wakilai na tara.

Hakan na zuwa ne duk da cewar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki ta tsayar da Shugaban masu rinjaye a majalisa, Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin zabinta.

Da suke jawabi a taron manema labarai na hadin gwiwa a jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu a Abuja, Shugaban kungiyar na kasa, Kwamrad Adnan R. Ali; babban sakataren kungiyar na kasa, Kwamrad Baffo Umar; da kuma Daraktan labaran kungiyar, Mista Jibrin Danpullo, sunyi Magana akan jajaircewa, da kokarin Wase, wanda ke wakiltan mazabar Wase da ke jihar Plateau tun a shekarar 2007, da kuma kasancewarsa dan majalisa mai kwazo da kokari.

A cewarsu, sabanin sauran hukumomi, shugabancin majalisun dokokin kasar biyu na kebabbun mutane ne masu tarin kwazo da kokari.

Kakakin majalisa: Kungiyar matasa sunce lallai Wase ne zabinsu

Kakakin majalisa: Kungiyar matasa sunce lallai Wase ne zabinsu
Source: Facebook

Sun bayyana cewa Wase mamba ne mai biyayya ga APC a jihar Plateau, kuma yana shugabanci mai cike da nagarta, duba ga shirin tallafi da ya ba matasa da dama, sannan kuma ya bayar da kwangiloli daa dama domin amfanin al’umman mazabarsa.

KU KARANTA KUMA: Tinubu na mutunta ni a matsayin dan Buhari ta fuskacin siyasa – Bello

Don haka sun bukaci kwamitin iyayen jam’iyyar APC na kasa fa su sake tunani sannan su mika mukamin kakakin majalisa ga yankin arewa ta tsakiya wacce bata taba samar da kakakin majalisa ba tunda aka samu damokradiyya a 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel