Sarkin musulmi ya nada Sadaukin Sakkwato a karo na farko

Sarkin musulmi ya nada Sadaukin Sakkwato a karo na farko

-Sarkin musulmi ya nada Mallam Lawal Maidoki sarautar da ba a taba nadama wani ita ba

-A karo na farko an nada Sadaukin Sakkwato a fadar mai alfarma Sarkin musulmi

A ranar Juma’a ne Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya nada Mallam Lawal Maidoki a matsayin Sadaukin Sakkwato. Muhimman mutane daga ciki da wajen Najeriya sun halarci wannan nadi wanda akayi a fadar Sarkin musulmin dake Sakkwato.

Bukin ya kayatar kwarai saboda shine irinshi na farko da aka taba yi a tarihin masaruatar. A nada sarautar Sadauki, kalmar dake nufin mai yiwa mutane hidima. Wanda aka nadan ya kasance mamba ne na kungiyar koli kan harkokin addinin musulunci ta kasa, jagoran kungiyar da’awar addinin muslunci ta kasa da kuma shugaban kwamitin zakka da wakafi na jihar Sakkwato.

Sadaukin Sakkwato na farko

Sadaukin Sakkwato na farko
Source: Twitter

KU KARANTA:Gangamin masu laifi a Afrika ta yamma, Hukumar Yan sandan kasa da kasa tayi gargadi

Sarkin musulmin da yake bada tsokaci akan wanda aka nadan yace, malamin addinin ya samu yabo daga wajen mutane da dama sakamakon jajircewarsa domin yiwa al’umma aiki ba tareda nuna gazawa ba ko kyashi.

“Maidoki ya bada gudumuwar da ta zarce misali domin kawowa al’umma abubuwan cigaba musamman harkokin da suka shafi addini wanda ya kasance yana yi tun daga yarintarsa har zuwa yanzu kuma bai fasa ba.”

Shi kuwa gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal ya fadi maganganu na yabo ga Mallam Maidoki inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai matukar kaunar cigaban addinin musulunci a jihar dama kasa baki daya.

“Da dama daga cikinmu sun koyi abubuwa daban-daban daga rayuwarsa,” inji gwamnan.

Da yake bada nashi bayani wanda aka nadan cewa yayi, “babu abinda zan ce face in mika godiyata ga Allah (SWT) wanda cikin iyawarsa Ya bani damar samun wannan matsayi. Ina kuma fatan Allah Ya bani ikon sauke nauyin da ya karu a bisa kaina.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel