Kasar Kamaru za ta dawo da yan Najeriya 4,000 gida

Kasar Kamaru za ta dawo da yan Najeriya 4,000 gida

A ranar Laraba, jami'an gwamnatin kasar Kamaru ta yanke shawara da gama shirye-shiryen dawo da yan Najeriya masu gudun hijra 4,000 a kasar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu, 2019.

Game da cewar gwamnan jihar, Midjiyawa Bakari, yan gudun hijran dake sansanin Minawao, suka amince da kansu cewa za su dawo gida.

"Mun yi yarjejeniya da gwamnatin Najeriya kan dawo da yan gudun hijra 4,000 daga jihar Adamawa zuwa Najeriya."

"Wadannan ne na farko da zamu dawo da su amma zamu cigaba da dawo da sauran" Bakari ya bayyanawa manema labarai.

Kasar Kamaru za ta dawo da yan Najeriya 4,000 gida
Kasar Kamaru za ta dawo da yan Najeriya 4,000 gida
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari zai sallami dukkan ministocinsa

A cewarsa, za'a dawo dasu ta jirgin sama, kuma kasar Kamaru za ta samar tsaro ga yan gudun hijran daga sansanin gudun hijran zuwa filin jirgin sama.

"Muna (Najeriya da Kamaru) tattaunawa kan yadda zamuyi da yaransu da suka fara zuwa makaranta a nan da kuma dukiyoyin da suka mallaka a nan,"

A watan Afrilu, kasar Kamaru ta taimakawa yan gudun hijra 40,000 daga cikin 60,000 da suka gudu zuwa kasar Kamaru gabanin zaben 2019 wajen dawo dasu gida.

Game da cewar majalisar dinkin duniya, sansanin Minawao na dauke da yan gudun hijran Najeriya 57,000 da suka arce daga kasar sakamakon rikicin Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel