Shettima ya ziyarci iyalan marigayi Mamman Nasir

Shettima ya ziyarci iyalan marigayi Mamman Nasir

Gwamnan jihar Borno kuma Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Kashim Shettima a jiya Talata, 16 ga watan Afrilu ya kai ziyara garin Malumfashi, jihar Katsina domin yin ta’aziya ga iyalan marigayi jigon arewa kuma tsohon Shugaban kotun daukaka kara, Justis Mamman Nasir wanda ya rasu a ranar Asabar.

Kakakin Shettima, Isa Gusau, ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Talata.

Yace a gidan iyalan marigayin, Shettima ya samu tarba daga Alhaji Ahmed Adulkadir tare da dattawa da sarakuna da dama.

Shettima ya ziyarci iyalan marigayi Mamman Nasir

Shettima ya ziyarci iyalan marigayi Mamman Nasir
Source: Facebook

Yace gwamnan ya kuma gana da iyala marigayi Galadima, mata, a fadar sarki tare da wasu tawagarsa da suka yi addu’o’i ga marigayin da kuma iyalansa.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama yan fashin da suka addabi mutane a hanyar Zaria-Kaduna

A baya Legit.ng ta rahot cewa an haifi Jastis Nasir a shekarar 1929 a jihar Katsina. Ya yi karatun makarantar sakandire a Kaduna, inda ya samu takardar shaidar kammala karatun sakandire ta kasashen yammacin Afrika (WAEC) a shekarar 1947.

Marigayin ya halarci jami'ar Ibadan kafin daga bisani ya wuce kasar Ingila, inda ya kammala karatunsa na digiri a bangaren shari'a a shekarar 1956.

Bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 1956, an nada shi a matsayin alkali kafin daga bisani a nada shi a matsayin minista shari'a, na yankin arewacin Najeriya, a shekarar 1961, mukamin da ya rike na tsawon shekaru biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel