Mai rabo ka samu: Hukumar kwastam ta bude sahafin daukan manyan ma'aikata 3,200

Mai rabo ka samu: Hukumar kwastam ta bude sahafin daukan manyan ma'aikata 3,200

Shugaban hukumar kwastam na kasa (CGC), Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya ce hukumar kwastan (NCS) za ta bude shafin ta na yanar gizo daga karfe 12:00 na safiyar ranar Laraba domin bawa masu sha'awar aiki da hukumar damar nuna sha'awar su ta cike gurbin ma'aikata 3,200.

Ya ce za a bude shafin ne na tsawon sati uku domin masu sha'awar aiki da hukumar kwastam a matakin manyan jami'ai su cike bayanansu tare da aika takardun su.

Kanal Ali, wanda mukaddashin mataimakinsa mai kula da sashen albarkatun mutane, Sanusi Umar, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a yau, Talata, a Abuja. Ya ce daukan sabbin ma'aikatan ya biyo bayan amincewar kwamitin zartar wa na gwamnatin tarayya, kuma za a dauki ma'aikatan ne bisa tsarin hukumar raba dai-dai a aiyukan gwamnatin tarayya (FCC).

Mai rabo ka samu: Hukumar kwastam ta bude sahafin daukan manyan ma'aikata 3,200

Hameed Ali yayin gabatar da jawabi ga jami'an kwastam
Source: Depositphotos

Da ya ke karin bayani a kan daukan sabbin ma'aikatan, Kanal Ali ya ce za a dauki ma'aikata 800 a matakin 'superintendent', yayin da za a dauki mutum 2,400 a bangaren 'Insfekta' da bangaren kananan mataimaka.

Ya ce, domin tabbatar da cewar 'yan Najeriya sun samu labarin daukan ma'aikatan da hukumar za tayi, an saka sanarwa a manyan jaridun kasa guda 7.

DUBA WANNAN: An samu 'sa hannun' mace a kan takardar Naira a karo na farko cikin shekara 59 da wanzuwar Najeriya

Ya bayar da adireshin yanar gizo da masu sha'awar neman aikin zasu bayar da bayanansu kamar haka: www.vacancy.customs.gov.ng.

Kaxalika ya gargadi masu neman aiki da hukumar ta kwastam da su kula da 'yan damfara, wadanda zasu karbi kudinsu da sunan za su samar masu aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel