Sojoji sun yiwa gari a Zurmi zobe, sun hallaka yan bindiga da dama, sun damke wasu

Sojoji sun yiwa gari a Zurmi zobe, sun hallaka yan bindiga da dama, sun damke wasu

Wasu yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara sun gamu da ajalinsu yayinda jami'an sojin Najeriya suka kai mumunan hari garin Tsaru dake karamar hukumar Zurmi na jihar ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu, 2019.

Mazauna garin sun laburta cewa sojojin sun dira ne misalin karfe 1 na rana kuma suka zagaye garin kafin karasawa cikin garin.

Wani mai idon shaida yace: "Yayinda wasu sojojin ke zagaye da hanyar shiga da fita daga garin, wasu sun shiga cikin kasuwar garin domin neman yan bindiga wadanda ke yawo da makamansu a fili. Sun kashe da yawa, yayinda wasu suka jefar da makamansu suka arce."

"Ba zan iya cewa ga adadin wadanda aka kashe ba, amma an kashe da yawa daga cikinsu kuma wasu sun gudu da raunuka. Lokacin da sojin suka zo, ba wuya sun gane yan bindigan saboda suna rataye da makamansu a kafada."

"Mun ga yan bindiga hudu da aka kama. Daya daga cikinsu mai sayar da magani ne a garin, ya kasance shine mai samawa yan bindigan magani."

KU KARANTA: Za muyi duk mai yiwuwa Ali Ndume ya janyewa Ahmad Lawan - Kashim Shettima

Kakakin hukumar soji a jihar Zamfara, Clement Abiade, ya tabbatar da wannan rahoto amma yace har yanzu ana cigaba da kai harin saboda haka ba zai iya magana a kai ba.

Mun kawo muku labarin cewa wasu yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara sun dawo cin karansu ba babbaka a cikin garururuwan karamar hukumar Zurmi na jihar bayan hukumar soji ta fara kai hare-hare dazukan da yan bindigan ke boyewa.

Wasu mazauna garin sun bayyana cewa tun lokacin da soji suka fara kai hare-hare cikin dazuka, yan barandan jihar sun guje daga dazukan zuwa cikin gari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel