Wata uwar yara 8 mai shekara 45 ta samu digiri na uku daga jami’ar Usman Dan Fodio

Wata uwar yara 8 mai shekara 45 ta samu digiri na uku daga jami’ar Usman Dan Fodio

- Wata uwar yara 8 mai shekara 45, Halima Usman ta samu digiri na uku daga jami’ar Usman Dan Fodio

- Halima wacce ta kasance yar asalin jihar ta samu wannan digirin ne a fannin lissafi

- Gwamnatin jihar Kebbi ce ta bayyana wannan abun alfaharin a shafinta na Twitter domin taya ta farin ciki

Wata mata yar shekara 45 wacce ta haifi yara takwas daga jihar Kebbi, Halima Usman, ta kammala karamin digiri na uku a fannin lissafi.

An bayyana hakan ne a shafin Twitter na gwamnatin jihar Kebbi, @KBStGovt, a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu.

Legit.ng tattaro cewa Halima ta mallaki wannan kwali na digiri na uku ne daga jami’ar Usman Dan Fodio sannan an bata takardar ne a lokacin bikin yaye daliban makarantar na 2019.

Kalli hotunan a kasa:

Wata uwar yara 8 mai shekara 45 ta samu digiri na uku daga jami’ar Usman Dan Fodio
Halima Usman cikin shigarta na kammala karatu
Asali: Twitter

Wata uwar yara 8 mai shekara 45 ta samu digiri na uku daga jami’ar Usman Dan Fodio
Halima tare da wasu daga cikin yaranta
Asali: Twitter

Wata uwar yara 8 mai shekara 45 ta samu digiri na uku daga jami’ar Usman Dan Fodio
Halima tare da wani da ake ganin mijinta nee
Asali: Twitter

A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta ruwaito cewa wata mata mai suna Ochuwa Momoh George, mai yara hudu, ta samu digiri na uku daga jami’ar Lagas.

KU KARANTA KUMA: Fashi: Ministan tsaro yace furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya

Matar wacce ta cika da farin ciki ta je shafin Facebook domin bayyana farin ciki a wannan tafiya tata na mallakar takarar da sakamako mafi daraja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel