A baiwa ma'aikatanmu daman rike makamai - Hukumar FRSC

A baiwa ma'aikatanmu daman rike makamai - Hukumar FRSC

Shugaban majalisar amintattun hukumar kare hadura wato Federal road safety commission (FRSC), Mallam Buhari Bello yayi kira ga gwamnatin Nigeria akan ta samar ma ma’aikatan ta makamai wanda zasu taimaka wurin gudanar ta aiyukan su da kuma kare kansu.

Ya bayyana hakane jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja bukin kaddamar da sabbin motocin sintiri guda 77, yace ta’addanci da hare haren da ake kaima maikatansu yayin gudanar da aiyukan su abin al’ajabi ne.

Yace harin yana kai ga sunji munanan raunuka, rasa rayukansu da kuma lalacewar makaman su.

Yace motocin sintirin da aka kaddamar ga hukumar sun zo ne daga karkashin gwamnatin Nigeria dan kwarin gwiwar aikin su.

KU KARANTA: A sabon gwamnati, Ministoci daya ko biyu kawai zasu dawo – Majiya daga Aso rock

A bangaren shugaban hukumar FRSC, Dr.Boboye Oyeyemi yace duk lokacin da jami’an suka sanya motoci masu yawa aikin su yana bunkasa.

A bangare guda, Hukumar FRSC ta gargadi jami'anta ne sanadiyar wani hadari da ya auku ranar Juma'a a garin Ibadan sakamakon biyo masu laifi da jami'an hukumar su kayi

Hukumar tayi wannan gargadin ne ranar Assabar da cewa jami’anta su daina bin masu laifi a guje ko ma menene laifin da suka aikata.

Jami’i mai kula da sashen ilmantar da jama’a na hukumar, mai suna Bisi Kazeem ne ya bada wannan sanarwa yayinda yake ganawa da manema labarai a Legas ta wayar tarho.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel