Rikicin Zamfara: An ga sanannun yan bindiga a gidan bikin 'yayan Sarkin Zurmi kuma sun bada gudunmuwa

Rikicin Zamfara: An ga sanannun yan bindiga a gidan bikin 'yayan Sarkin Zurmi kuma sun bada gudunmuwa

Bayan zargin da ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, yayi kan sarakunan gargajiyan jihar Zamfara, wani mazauni ya bayyana abinda suka gani a daurin auren 'yayan sarkin Zurmi.

Jaridar Premium Times ta samu rahoton wani mazauni wanda yayi kira ga gwamnati ta tattauna da sarakunan gargajiya saboda akwai alaka tsakanin wadannan yan bindigan da wasu sarakuna a jihar.

A cewarsa, "A shekarar 2016 lokacin da sarkin Zurmi, Atiku Abubakar, ya aurar da 'yayansa mata guda hudu, kusan dukkan shararrun yan bindigan da aka sani sun halarci taron bikin kuma su suka bayar da gudunmuwan dabbobin da aka yanka a bikin."

"A lokacin bikin, an gayyaci wani shahrarren mawakin barayi, Sani Danyaya, daga kasar Nijar. Ya kwashe kwanaki biyu yana yiwa yan bindigan waka tare da karuwansu a garin Zurmi, hedkwatan karamar hukumar Zurmi."

KU KARANTA: Sakamakon harin Soji, yan bindigan sun dawo cikin gari - Mazauna sun laburta

Ya ce duk da cewa karamar hukumar Zurmi tana fama da wannan kalubale, wannan fito-na-fito da Sojoji suka da yan bindigan ba zai yi tasiri ba sai an tura sojojin kasa cikin garin Zurmi saboda mutane na shirye da bayyana musu yadda yan bindigan ke gudanar da tafiye-tafiyensu.

A baya, LEGIT.NG sun bada rahoto a makon da ya gabata cewa ministan tsaro, Mansu Dan Ali, a wata jawabi ya ce rahoton leken asiri ya nuna cewa wasu manyan sarakunan gargajiya na da hannu cikin wannan kashe-kashe da ke faruwa a arewacin Najeriya.

Amma majalisar sarakunan gargajiyan jihar sun nuna bacin ransu kan wannan jawabin inda suka kalubalancesa da ya ambaci sunayen sarakunan da yake nufi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel