Tirkashi: An kama tsohon shugaban karamar hukuma da laifin zina da matar makwabcin sa

Tirkashi: An kama tsohon shugaban karamar hukuma da laifin zina da matar makwabcin sa

A ranar juma'a ne yan sandar jihar Jigawa suka bayyana cewa sun kama tsohon shugaban karamar hukumar Kafin Hausa dake jihar Jigawa,wanda ake kira da Aliko Kwatalo da laifin zina da matar aure.

Abin ya faru ne a ranar talata a NTA kwatas dake hanyar Garin Gabas a kamar hukumar Hadejia na jihar.

Mijin matar wanda ake kira Danliti Abubakar ne ya kai kara wurin yan sanda.

KU KARANTA: An kama wasu daliban jami’a 2 suna zanama wani jarabawar JAMB

Yace: "Na ji sanda uwargidata take shirya inda zasu hadu dashi a wayar tarho a lokacin da yake niyyar barin gidansa. Wannan shi ya sa nake zarginsa."

“Bayan na gama jin abinda suka shirya sai nayi kunnan shegu kamar ban jiba illa sai na boye, kafin na ankara sai naga malam Kwatalo ya sullubo cikin gidana. Da ganin haka sai na kulle kofar waje ta baya sai na kira yan agaji, yan sanda da sauran makwabta na kusa dan a kamashi”.

Mazajen makwabtan juna ne cewar yan sandan. Kakakin dan sandan, Audu Jinjiri ya shaida da haka.

Yace: "An kama wanda ake zargin kuma za'a mika shi kotu.”

Dan sandan ya bayyana cewa matar ta karya kafarta daya yayin da take yunkurin guduwa.

Ya kara da cewa matar mai suna Fatima Usman yar shekara Ashirin da biyar ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel