An tura wasu mutum biyu gidan kaso saboda dukan wata mata da su kayi

An tura wasu mutum biyu gidan kaso saboda dukan wata mata da su kayi

- Wasu matasa biyu sunyi ma wata mata duka, sanadiyar hakan kuwa sun tsinci kansu a gidan yari da daurin shekara daya.

- Bayan duka da sukayiwa matar sunyi mata kwacen kudi da kuma wayarta ta hannu kirar kamfanin Itel.

Wata kotun majistiri dake garin Jos ranar Juma’a ta tura da wasu mutum biyu zuwa gidan yari na tsawon shekara daya akan laifin duka da kuma kwancen wayar salula da sukayiwa wata mata.

Yan sanda sun kama mutunen biyu masu suna, Usman dan shekara 19 mai sana’ar tireda da Hamza mai shekara 20 wanda ke sana’ar kanikanci da laifin sata da kuma hadin gwiwa wajen aikata ta'asa.

Mizani

Mizani
Source: UGC

KARANTA WANNAN:Gwamnatin Tarayya na neman hanyoyin bunkasa samun kudin shiga - Udoma

Mai hukunci a kotun ta majistiri mai suna, Roseline Baraje ce ta yankewa Usman da Hamza hukunci bayan sun karbi laifin da ake tuhumarsu da shi. Baraje har wa yau ta basu damar fansar kawunansu akan kudi naira dubu ashirin da biyar daga ko wane dayansu.

Wanda ya amshi wannan karar mai suna, Ijuptil Thiawu ya fadawa kotun cewa an kawo wannan karar ne daga ofishin yan sanda wanda wata mata mai suna Esther wacce take zaune a titin Rukuba dake garin Jos ta shigar.

Thiawu yace wadanda ake tuhumar sun lakadawa ita matar dukan tsiyane inda kuma suka karbe mata wayarta kirar Itel wacce aka kiyasta kudinta naira dubu shida da kuma tsabar kudi naira dubu biyar wanda shima suka kwace daga hannunta.

Yace a dai dai lokacin da yan sanda ke bincike an same su da wannan wayar tare da kuma kudin. Yace kuma kara da cewa wannan laifin da suka aikata yaci karo da sashe na 559,239 da kuma 272 dake cikin dokokin ‘Penal Code’.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel