NASFAT ta kulla alaka da makarantar koyar da yada labarai domin koyar da mambobinta

NASFAT ta kulla alaka da makarantar koyar da yada labarai domin koyar da mambobinta

-NASFAT zata horar da mambobinta akan harkokin yada labarai

-Makarantar koyar da aikin yada labarai a Legas zata horar da yan kungiyar addini ta Nasrul-lahi na tsawon kwanaki uku kacal

Sananniyar kungiyar addinin musuluncin nan wato NASFAT ta kulla alaka da makarantar koyar da aikin yada labarai mai suna ‘National Broadcast Academy, NBA’ ta Legas domin horar da mambobinta akan harkokin da suka shafi yada labarai saboda samun dammar cigaba da gudunar da da’awarsu cikin sauki.

Sakataren kungiyar mai kula da sahsen rubuce-rubuce, Banji Busari a cikin wani batu na shi yace, horon na kwana uku da aka tsara wanda za’a fara shi a yau din nan zai mayar da hankaline akan fannoni hudu wanda ya hada da labarai, rubutawa da kuma kawo rahoto, tsarin dokar aikin na yada labarai, gabatarwa da kuma jawabi gaban jama’a.

NASFAT
NASFAT
Asali: UGC

KARANTA WANNAN:Son kai kawai aka nuna a zaben gwamnan Kano - Abba Gida-Gida

Da yake jawabi, Daraktan NBA, Abiola ajibola yace wadannan fannoni da za’a koyar da mambobin a tsarasu ne tsaf domin basu damar gudanar da da’awarsu cikin sauki domin isar da sako zuwa ga sauran jama’a. Ya sake cewa lallai wannan horon sun shirya masa tsaf saboda akwai kwararru cikin shi wannan aiki da zasu kasance a wurin wannan taro na horarwa duk dan dai wanda zasu zo wurin wannan horon sun amfana kwarai da gaske.

Wadanda zasu halarci horon sun hada da, sakatarorin rubuce-rubuce, masu da’awa da kuma manyan masu mukamai na NASFAT da ma sauran wasu masana akan wannan aikin.

A wani labarin kuwa, hukumar INEC ta lashi takobin cewa lallai ba zata baiwa gwamanan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shahadar nasara a zaben majalisar dattawa ba.

Hukumar ta INEC tace sam Okorocha ba zai samu takardar shahadar ba daga wurinta saboda wasu hujjoji da take dasu akan gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel