Zaben gwamnan Sokoto: Kotu ta amincewa APC ta binciki kayayyakin zabe
- Kotun karbar korafe korafen zabe a jihar Sokoto ta amincewa APC ta binciki kayayyakin da aka gudanar da zaben jihar da su
- APC da dan takararta, Aliyu Sokoto, sun shigar da kara gaban kotun inda suke kalubalantar nasarar Aminu Waziri Tambuwal
- APC ta ce lauyoyinta na da sama da hujjoji 40 da zasu gabatar, tana mai cewa akwai hujjoji na cewar an tafka magudi a zaben gwamnan jihar
Kotun da aka kafa domin sauraron korafe korafen zaben gwamnan jihar Sokoto ta amince da wata bukata ta jam'iyyar APC, ta hannun lauyanta, Dr. Alex Iziyon SAN, na barin jam'iyyar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zabukan jihar na ranar 9 da 23 ga watan Maris.
Jam'iyyar APC da dan takararta, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto, sun shigar da kara gaban kotun inda suke kalubalantar nasarar da gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP ya samu.
Wani mamba a tawagar lauyoyin jam'iyyar da ke jihar, Mr. Bashir Muazu Jodi, a madadin babban lauyan, Izinyon SAN, ya bayyana hakan ga manema labarai a Sokoto a ranar Alhamis bayan zaman kotun.
KARANTA WANNAN: Zaben gwamnan Rivers: Kotun koli ta yi watsi da bukatar APC na kan sanya 'yan takara
Jodi ya ce lauyan na da sama da hujjoji 40 da zai gabatarwa kotun a lokacin da aka soma shari'ar, yana mai cewa akwai hujjoji na cewar an tafka magudin da har ya baiwa Tambuwal nasara, musamman karya dokar zaben kasar ta 2010 kamar yadda aka sabunta, a zaben gwamnan jihar zagaye na biyu da kuma zaben jihar na farko.
Wadanda ake tuhumar dai sun hada da Tambuwal da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da kuma jam'iyyar PDP.
A cewarsa, za a aikewa wadanda ake karar takarda, wacce za su mayar da amsa a cikin makwanni biyu, bayan nan ne kuma kotun za ta sanya ranar fara sauraron shari'ar.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng