Kana da labarin Matar da tafi kowacce mace arziki a duk fadin Najeriya?

Kana da labarin Matar da tafi kowacce mace arziki a duk fadin Najeriya?

Tabbas arziki na Allah ne, Ya kan baiwa duk wanda Yaso a lokacin daya so, kuma Ya hana duk wanda yaso ba don baya sonsa ba, don haka sai kaga a gida daya amma an samu wani talaka wani kuma attajiri, Ikon Allah mai duka kenan.

A yau Legit.ng ta kawo muku labarin hamshakiyar attajira kuma gawurtacciyar yar kasuwar Najeriya da tafi fice a harkar juya kudi wanda yasa ta zamto macen da tafi arziki a Najeriya, a wani kaulin ma a duk fadin Duniya babu mace bakar fata dake da arzikinta, Uwargida Funsho Alakija.

KU KARANTA: Gani ga wane: Fusatattun matasa sun kona wani dan fashi kurmus

Kana da labarin Matar da tafi kowacce mace arziki a duk fadin Najeriya?
Alakjia
Asali: Depositphotos

Ga dai wasu muhimman abubuwa game attajira Funsho Alakija kamar haka;

- An haifi Folorunsho Alakija a ranar 15 ga watan Yulin shekarar 1951

- Alakija yar kabilar Yarbawa ce daga jahar Legas

- Tsohuwar Tela ce, kuma har yanzu tana sana’ar dinki

- Ita ce shugabar kamfanin hakar danyen mai da sarrafa man fetir na FAMFA Oil

- Kamfanin FAMFA na samar da ganga 250,000 na danyen mai a duk rana

- Arzikin Alakija ya kai dala biliyan 1.6, kimanin naira biliyan 576 kenan

- Ita ce ta 1561 a jerin masu kudi biloniya na Duniya gaba daya

- Tana da jirgin yawo da kudinsa ya kai dala miliyan 46

- Tana da gidauniya dake tallafa ma mata, marayu da zawarawa

- Tana da Miji, Modupe Alakija, kuma suna da yaya guda hudu

A wani labari makamancin wannan kuma, a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu ne hamshakin attajirin nan dan asalin jahar Kano, kuma wanda yafi kowa kudi a nahiyar Afirka gaba daya, Aliko Dangote ya cika shekaru 61 a duniya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng