Duniya labari: Kudan Zuma ta kai hari Legas, ta kashe jami'in Kwastam yana aiki

Duniya labari: Kudan Zuma ta kai hari Legas, ta kashe jami'in Kwastam yana aiki

Rahotanni sun bayyana cewa wani babban jami'in Kwastam ya gamu da ajalinsa bayan da gungun kudan Zuma suka kai masa hari a yayin da ya ke bakin aiki. Jami'in, Abba Abubakar, ya mutu ya bar matarsa da 'yaya da dama.

Abba Abubakar, jami'in hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam) da ke aiki a ofishin hukumar da ke Seme, kan titin Ashipa, Badagry, jihar Legas, ya gamu da ajalinsa a ranar Talata bayan da wasu gungun kudan Zuma suka kai masa hari.

"Cikin kaduwa da jimami, hukumar yaki da fasa kwabri ta kasa reshen Seme ke sanar da mutuwar ma'aikacinmu, CSC Abba, A.," a cewar mai magana da yawun hukumar reshen Seme, Saidu Abdullahi a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Shugaban kasar Sudan ya yi murabus bayan shekaru 30 a kujerar mulki

Duniya labari: Kudan Zuma ta kai hari Legas, ta kashe jami'in Kwastam yana aiki

Duniya labari: Kudan Zuma ta kai hari Legas, ta kashe jami'in Kwastam yana aiki
Source: Getty Images

Mr Abdullahi ya bayyana mamacin a matsayin jami'in da ke gudanar da ayyukansa kamar yadda ya dace.

"Bai taba fashin zuwa aiki ba a kowacce rana. Muna matukar jimamin rasa wannan gwarzon jami'i," a cewar Mr Abdullahi.

Jami'in, wanda haifaffen jihar Yobe ne, ya mutu ya bar matarsa da yara da dama.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel