Jami'an yan sanda sun damke yan fashi 60

Jami'an yan sanda sun damke yan fashi 60

Hukumar yan sandan brnin tarayya ta yi ikirarin damke wasu mutane da ake zargi da fashi da makami 60.

Mataimakin kwamishanan yan sanda dake shugabantan sashen binciken yan baranda, Salisu Gyadi-Gyadi ya bayyana hakan ne yayinda yake hira da manema labarai ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2019.

Daga cikin wadanda aka kama sune Rabiu Usman, Bala Abba, Aminu Mohammed, Bilyaminu Abubakar , Nuhu Ahmed, Aminu Musa, Sani Wanzam, Abdulsalam Isyaku, Magaji Amadu, Aminu Danjuma, Emmanuel David, da wasu 24.

Ya bayyana cewa an samu abubuwa irinsu: kwalaben Kodin 43, wukake 12, adduna 2, sanduna 14, kayayyakin tsubbu, guduma 3, wayoyi 16, harsasan AK 47 9, da ganyen wiwi.

Ya ce sun damke wadannan yan barandan ne bisa ga rahoton leken asiri da hukumar ta samu.

Yace: "Ina mai sanar da ku cewa matakan da muka dauka domin kawar da barandanci a birnin tarayya ya fara haifar da 'da mai ido.

"Hukumar na alfaharin bayyanawa cewa nasarorin da ta samu sakamakon rahotanni da muka samu daga wajen alummar unguwa."

Kwamishanan ya ce hukumar ta yi kokari wajen damke wasu da suka are kuma za'a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel