Matsalar tsaro na da alaka da matsalar fannin ilmi – Inji Saraki

Matsalar tsaro na da alaka da matsalar fannin ilmi – Inji Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa samar da ingantaccen ilmi na daya daga cikin muhimman matakan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kyakkyawan tsaro a cikin al’umma.

Hakan ya sa Saraki danganta matsalar tsaro a kasar nan da kalubalen da fannin ilmin kasar ke fuskanta.

Saraki ya yi wannan jaawabi ne a wajen taron Kungiyar Shugabannin Majalisar Dattawa ta Duniya, a Doha, babban birnin kasar Qatar. Taron dai shi ne na 140.

Hadimin Saraki, Sanni Onogu, ya bayyana cewa Saraki yace muddin aka bai wa matasa ingantaccen ilmi, to za a dakile yawaitar matasa masu tsatstsauran ra’ayin da ke kai su ga shiga kungiyoyin ta’addanci.

Matsalar tsaro na da alaka da matsalar fannin ilmi – Inji Saraki

Matsalar tsaro na da alaka da matsalar fannin ilmi – Inji Saraki
Source: Twitter

Ya ce idan aka ginganta ilmi, to al’umma ta gari za ta wanzu tare da rayuwar zaman lumana da cigan kasa.

“Shirin Afuwar Shugaban Kasa ga tsagerun Neja Delta ya yi tasiri sosai. Don ya samar wa matasa guraben karatu, tare da daukar nauyin su jar zuwa jami’o’i.”

Haka kuma shirin cin gajiyar afuwar ya haifar da zaman lafiya a yankin, saboda matasa sun yi watsi da tsageranci, sun kama karatu gadan-gadan.

Ya ce Majalisar Dattawa ta Najeriya ta yi rawar gani a fannin ilmi, inda ta yi gyara ga dokar UBEC, wato wajibcin samar da ilmi kyauta ga yara har zuwa sakandare.

Sannan kuma ya ce an gyara dokar ta UBEC, yadda jihohi za su ji sauki karbar tallafin kudaden Hukumar Samar Da Ilmin Bai-daya, wato UBEC.

KU KARANTA KUMA: Kin rattaba hannu a kan wasu dokoki 2: Majalisa za tayi amfani da karfin ikonta a kan Buhari

A wani lamari kuma, Legit.ng ta rahoto cewa majalisar dattawa a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu tayi Allah wadai da kasha-kashen Zamfara, sannan ta yabi yan Najeriya akan fitowa da suka yi kwansu da kwarkwatansu don taya al’umman jihar yin zanga-zanga.

Yayinda Sanata Kabiru Garba Marafa (APC, Zamfara) ya gabatar da lamarin, Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zo da wani shiri na shekaru 10 don kula da yan gudun hijira a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel