Gani ga wane: Yadda kotu ta garkame mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama'a

Gani ga wane: Yadda kotu ta garkame mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama'a

- Wata kotun majistire ta yankewa wasu mutane tara watanni shida a gidan kaso, bayan kamasu da laifin yin ba-haya a bainar jama'a

- Daga cikin laifukan da ake zargin mutanen sun hada da rashin makewayi a gidajensu, rashin mazubin shara da kuma yin ba-haya a bainar jama'a

- Sai dai, ya basu zabi, na biyan tarar N5,000 zuwa N15,000

Adeosun Abayomi na wata kotun majistire da ke Aramoko, ya yankewa wasu mutane tara watanni shida a gidan kaso, cikinsu kuwa har da wani mai rike da sarautar gargajiya da ma'aikacin gwamnati, bayan kamasu da laifin yin ba-haya a bainar jama'a.

Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Olaleye Isaac, Ologun Ala, Agboola M, Atoro, Adetoyinbo, Adesoba Sunday, Jacob Taiwo, Titus Ibironke da Olu Obateru, dukkaninsu mazauna karamar hukumar Ekiti ta Yamma da ke cikin jihar Ekiti.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ya ruwaito cewa wadanda aka yankewa hukuncin an gurfanar da su gaban kotun ne bisa zarginsu da aikata laifuka da dama da suka shafi karya tsaftar muhalli, rashin makewayi a gidajensu, rashin mazubin shara da kuma yin ba-haya a bainar jama'a.

KARANTA WANNAN: Cikin kwanaki 60: Kotu ta umurci hukumar NIS da ta biya wani tsohon ma'aikacinta N9.7m

Gani ga wane: Yadda kotu ta garkame mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama'a
Gani ga wane: Yadda kotu ta garkame mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama'a
Asali: Twitter

Da ya ke yanke hukunci, Mr Abayomi ya bayyana cewa sun gurbatar da muhalli ta hanyar yin kashi a bainar jama'a.

Sai dai, ya basu zabi, na biyan tarar N5,000 zuwa N15,000.

A wani labarin makamancin wannan, kotun majistiren ta bayar da umurnin cafko wasu mutane tara da suka gaza gurfana a gabanta, da ake zarginsu da aikata laifuka makamantan na sama.

Ya baiwa rundunar 'yan sanda umurnin gurfanar da su a ranar 25 ga watan Afrelu, domin yanke masu hukunci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel