Wata mata ta yanke jiki ta fadi yayinda take fada da kishiyarta a Kano

Wata mata ta yanke jiki ta fadi yayinda take fada da kishiyarta a Kano

- Wata mata ta yanke jiki ta fadi yayinda take fada da kishiyarta a Kano

- Lamarin mara dadin j ya afku ne a kauyen Jiramo da ke yankin karamar hukumar Takai a jihar

- Kakakin yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin

Wata mata mai suna Bilkisu Abubakar, ta yanke jiki ta mutu yayi da take fada da kishiyarta, Hajara Abubakar a jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa matayen biyu suna auren miji guda ne a kauyen Jiramo da ke yankin karamar hukumar Takai a jihar.

Wata mata ta yanke jiki ta fadi yayinda take fada da kishiyarta a Kano

Wata mata ta yanke jiki ta fadi yayinda take fada da kishiyarta a Kano
Source: UGC

Kakakin rundunar yan sanda, reshen Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da lamarin ga majiyarmu, yace lamarin ya auku ne a makon da ya gabata da misalin karfe 10 na dare.

KU KARANTA KUMA: Zamfara: Za mu ba gwamnatin tarayya hadin kai – Shugaban kungiyar masu hakar ma’adinai

Yace hakimin Fajewa, Alhaji Ya’u Hamza tare da wacce ta aikata laifin, Hajara sun tafi ofishin yan sanda, inda ya kai rahoton lamarin zuwa ga yan sanda.

Yace a halin yanzu an kai gawar marigayiyar asibiti.

A bangare guda kuwa, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani abin mamaki da ya faru a jiya Talata 9 ga watan Afrilu, a wani injin cire kudi (ATM), na wani banki a kusa da gidan rediyon Najeriya, da ke Dugbe, cikin jihar Ibadan, inda aka kama wani matashin yaro yana cire kudi a injin cire kudin ba tare da amfani da katin cire kudi ba.

Matashin yaron, mai suna Azeez Morufu, ya ce ba wannan ne karo na farko da ya fara cire kudi ba tare da katin cire kudin ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel