Kakakin majalisar wakilai: Dattawan Arewa ta tsakiya sun goyi bayan Idris Wase

Kakakin majalisar wakilai: Dattawan Arewa ta tsakiya sun goyi bayan Idris Wase

- Dattawan Arewa ta tsakiya sun bayyana matsayarsu na goyon bayan Idris Wase, a matsayin kakakin majalisar a zuwan majalisar ta tara

- Kungiyar ta ce tana da tabbacin cewa Umaru Bago, wani mai neman kujerar daga shiyyar zai hakura da takararsa ya barwa babban yayansa

- Sai dai wannan matakin da kungiyar ta dauka ya sabawa zabin jam'iyyar APC, wacce ta bayyana Gbajabiamila a matsayin wanda ta ke so ya gaji Dogara

Dattawa karkashin kungiyar dattawan Arewa ta tsakiya sun bayyana matsayarsu na goyon bayan tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Idris Wase, a matsayin kakakin majalisar a zuwan majalisar ta tara.

Kuyngiyar ta bayyana hakan a ranar Talata a wajen wani taron manema labarai a aBUJA.

Muhammadu Ari-Gwaska, wanda ya yi jawabi a madadin kungiyar, ya ce bayan gudanar da bincike, kungiyar ta yanke hukuncin goyon bayan Wase duba da irin kololuwar matsayinsa.

Ya ce yana da tabbacin cewa Umaru Bago, wani mai neman kujerar daga shiyyar zai hakura da takararsa ya barwa babban yayansa.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Shugaba Buhari makaryaci ne, ina da dalilan fadin hakan - Omokri

Kakakin majalisar wakilai: Dattawan Arewa ta tsakiya sun goyi bayan Idris Wase

Kakakin majalisar wakilai: Dattawan Arewa ta tsakiya sun goyi bayan Idris Wase
Source: Depositphotos

Ya kuma kara da cewa shiyyar Arewa ta tsakiya, duk da zaman lafiyar da take ci da dumbin ci gaba, na zama a koma baya wajen rabon mukaman siyasa.

Ya kuma roki shuwagabannin jam'iyyar APC da su baiwa shiyyar kujerar kakakin majalisar wakilan tarayyar duba da irin dabbaka demokaradiyya da ake yi a shiyyar.

Wannan kuwa a cewarsa idan har aka yi zai kara tabbatar da adalci, hadin kai, jin kai da kuma rashin nuna banbanci da jam'iyyar kullum ke nasiha akai.

Mr. Wase, wanda dai har yanzu bai bayyana kudurinsa na tsayawa takarar kujerarba a fili, zai fuskanci abokanansa a majalisar a wajen takarar kujerar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel