Davido,Olamide da YCEE na burgeni ,in ji yaron Wizkid

Davido,Olamide da YCEE na burgeni ,in ji yaron Wizkid

Shigar Davido, Olamide da YCEE na burgeni, inji dan shahararren mawaki Wizkid

Duk da cewa akwai zuwa makaranta da kuma wasu al’amura da kan iya shiga cikin ayyukan yau da kullum na mutane, da yawa daga cikin manyan mutane na ganin kasuwanci a matsayin abu na karshe wanda yaro zai yi tunaninsa.

Majiyar Legit.ng tace: Amma sai dai Boluwatife Balogun, dan Wizkid na farko, ya nuna kudurinsa na son fara sana’ar tsutura da wasu kayayyakin ado inda wannan yaro ya bayyana aniyarsa ta fara wannan sana’a inda yake kallon wasu jiga-jigan mawakan kasar nan a matsayin abin koyi ga sana’ar tasa.

Wizkid
Wizkid
Asali: UGC

KU KARANTA: Jami'ar UDUS za ta karrama Dangote da wasu Sarakunan Arewa biyu

A wata tattaunawa da akayi dashi wannan matashin yaro kuma Shugaban Czar da Czarina ya bayyana “babanshi daya daga cikin wadanda yakeso yayi masu sutura, Davido, Olamide da YCee sune sauran mutane ukun. Ya kara cewa wadannan sune wadanda nafi so a cikin mawakan Najeriya. Ina matukar son wadannan mawakan saboda sun kware a fanni wakokkin da sukeyi. Babu matsi a cikin aikin da sukeyi, inji shi.”

Duk da cewa dai ya fara ne da kayan kananan yara, mahaifiyarsa mai suna Shola Ogudugu ta bayyana mana cewa wannan kamfanin nasa nayin takalma da kuma kayan sawa na manya.

Ogudugu, wadda ta gabatar da bikin bude wannan kamfanin a ranar bikin zagayowar haihuwarsa a watan Mayun 2018, lokacin day a cika shekara bakwai, tace “Czar and Czarina an haifeshi a cike da burin samar da tufafi ga kananan yara abinda ya kasance an fara shi ne da Boluwatife. Mun fara ne da yi masa sutura shi kansa daga baya kuma muka samu cigabn yin suturar ga sauran mutane.”

“Boluwatife ya kasance yana zuwa da tsarin daban-daban masu kayatarwa sosai. Mutane na yawan tambaya a ina muke samo irin wadannan kayan ne, don haka sai muka maid a abin namu kasuwanci. Yaron shine dalilin assasa wannan kamfani. Shine dalilin samar da Czar da Czarina, ta kara cewa.”

“Ni kuma, nice daraktar kirkirar sabbin abububawa na kamfanin, shi kuma shine jigo kuma jagaban kamfanin. Kuma shine yake matsayin shugaban kamfanin da yake da ta cewa a kan abububawan da muka sarrafawa.”

Mutanen biyu sun nuna jin dadinsu ganin yadda kamfanin nasu ke bunkasa wanda har sunayiwa manyan jarumai a Najeriya da ma wasu kasashen Afrika kaya.

Kamfaninmu na dada daukaka da kuma samun karbuwa wurin mutane daga ko ina. "Munyi wa Bisola sutura, Terry G, YCee da ma wasu mutane da dama. Wani lokacin abin ma sai ya burgeka muna matukar jin dadin hakan kwarai da gaske,” suka ce.

Ogudugu ta fadi cewa babban bukin bude sashen yin suturar manya na nan tafe a Maison Fahrenheit hotel da ke Legas a ranar 19 ga watan Afirilu, wanda zai kasance daidai da zagayowar ranar haihuwarta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel