Barcelona ba sa'ar Manchester United bace, inji Deulofeu

Barcelona ba sa'ar Manchester United bace, inji Deulofeu

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Barcelona mai suna Gerard Deulofeu yanada tabbacin cewa Barcelona zata samu galaba akan takwararta wato Manchester United, yana mai cewa kungiyar dake kan gaba a gasar La Liga suna wani matakin daya zarce na kungiyar da Ole Solskjaer ke jagoranta.

Kungiyar kwallon kafar Manchester United zata fara karbar bakuncin zagayen wasar na farko ranar Laraba, wannan shi zai kasance haduwar wadannan kungiyoyin biyu na farko tun haduwarsu ta karshe da Barcelona ta lallasa United a wasan karshe na kofin zakarun nahiyar turai a shekarar 2011.

Zagayen wasar na biyu kuma za’a buga shi ne a Camp Nou filin Barcelona ranar 16 ga watan Afirilu.

Deulofeu

Deulofeu
Source: Getty Images

KU KARANTA: Marasa kishi ne masu bukatar a tuge Buratai –Odeyemi

Kungiyar dake taka leda a gasar Firimiya ta kasar Ingila sun samu cigaba tun lokacin da Solskjaer ya karbi ragamar jan akalar kungiyar daga hannun Jose Mourinho a watan Disembar da ya gabata ko da yake a yanzu suna fama ne da kyar inda suka sha kashi sau uku cikin wasanni hudu da suka fafata kwanan nan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel