Lafiya jari: Abubuwa 9 ya kamata ku sani game da cutar sankarau

Lafiya jari: Abubuwa 9 ya kamata ku sani game da cutar sankarau

Allah Ya kawomu lokacin zafi, wannan shine lokacin da mummunar cutar nan dake kashe mutane watau sankarau take bayyana, wanda zuwa yanzu ta kashe sama da mutane Arba’in da takwas daga watan Oktoban bara na 2018.

Haka ne yasa Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman bayanai game da wannan cuta, ta yadda jama’a zasu bi hanyoyin da suka dace don kauce ma kamuwa da cutar, da kuma neman hanyar samun waraka idan an kamu.

KU KARANTA: Gobara ta tafka mummunan barna a jami’ar Umaru Musa Yar’adua

- An samu rahoton sankarau sau 541 a jahohi 15 na Najeriya

- Sankarau na kama wani sashi na kwakwalwar dan Adam

- Tana sankarar da wuya, tare da kumbura kwakwalwa

- Tana sa karuwar dukan zuciyar dan Adam

- Tana matsanancin ciwon kai, amai da kasala

- Tana shafan lakkan dan Adam

- Ana iya dauka daga mutum zuwa mutum ta hanyar haduwar jiki

- Ana iya kauce mata ta hanyar tsaftace muhalli

- Ana iya yakarta ta hanyar allurar rigakafi da shan kwayoyi masu kare garkuwar jiki

Sai dai a yanayin zafin da ake ciki, jama’a na kokawa kwarai da gaske, wanda har ta kai ga wasu ma a waje suke kwana domin rashin wutar lantarki, yayin da wasu masu samun wutar suka ce fankar ma zafi take hurowa, kuma koda sun watsa ruwa, ruwan ma mai zafi ne.

A wani labarin kuma, masana kiwon lafiya sun bayyana cewa rashin tasan ma cutar da gaske da farkonta yasa take tasiri tsakanin al’umma, inda sai kaga wasu na zargin maita ko asiri aka yi musu, don haka ba zasu tafi asibiti ba har sai yaci ya cinyesu, inda masanan suka danganta hakan da jahilci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel