Da duminsa: Yan ta'adda da jami'an sa kai sun fafata a Katsina, 14 sun mutu

Da duminsa: Yan ta'adda da jami'an sa kai sun fafata a Katsina, 14 sun mutu

Rahotanni sun bayyana cewa kalla mutane 14 ne aka kashe a karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina, sakamakon wata arangama tsakanin 'yan ta'adda da jami'an sa kai na cikin gari da aka fi sani da 'yan bijilanti.

Lamarin dai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 14, rahotanni sun bayyana cewa ya faru ne a garin Tsamiyar Jino da ke karamar hukumar Kankara da ke Katsina.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Fashola ya dakatar da gina gidajen gwamnati a Abuja

SP Isah ya ce lamarin ya fara ne a lokacin da mambobin kungiyar 'yan bijilantin suka shirya kaddamar da kai hari a mabuyar 'yan ta'addan da ke cikin daji, inda suka kashe bakwai daga cikinsu, yayin da suma 'yan ta'addar suka bude wuta, inda suka kashe bakwai daga cikin 'yan bijilantin.

"Tuni DPO na 'yan sanda da ke a yankin ya isa idan lamarin ya faru, kuma an kwantar da tarzoma.

"An shawari mambobin jami'an sa kan da su daina daukar hukunci a hannunsu, su kasance masu neman hadin guiwar sauran jami'an tsaro da doka ta yarda da su, musamman su taimaka wajen bayar da bayanai da zasu kawo nasarar dakile ta'addanci da 'yan ta'adda," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel