An matsa wa Goje kan ya amince da Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

An matsa wa Goje kan ya amince da Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

- Wasu tsoffin gwamnoni na matsa wa tsohon takwaransu, Sanata Danjuma Goje, kan ya amince da Ahmed Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

- Ahmed Lawan ne dai zabin shugaban kasa Muhammadu Buhar da jam'yyar APC ma mulki

- Har ila yau Tsoffin gwamnonin APC cikin harda wasun su da ke rike da mukamin sanata, sun jaddada goyon bayansu ga hukuncin Buhari kan Lawan

Wasu tsoffin gwamnoni na matsa wa tsohon takwaransu, Sanata Danjuma Goje, kan ya amince da zabin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ahmed Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa.

An tattaro cewa Shugaban kasar ya gana da Goje akan lamarin.

Lawan, wanda ya kasance Shugaban masu rinjaye a majalisa, na ci giba da kamun kafa. A jiya Lahadi, ya gana da wasu zababbun sanatoci sannan ya roke su akan su bashi dama, jaridar The Nation ta ruwaito.

Tsoffin gwamnonin All Progressives Congress (APC), cikin harda wasun su da ke rike da mukamin sanata, sun jaddada goyon bayansu ga hukuncin Buhari kan Lawan.

An matsa wa Goje kan ya amince da Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa
An matsa wa Goje kan ya amince da Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa
Asali: Depositphotos

An tattaro cewa wasu daga cikin tsoffin gwamnonin sun hada da Ahmed Sani Yerima, Adamu Aliero, Abdullahi Adamu, Aliyu Wammako, Goerge Akume, Bukar Abba Ibrahim, Kabiru Gaya da kuma Godswill Akpabio.

KU KARANTA KUMA: Kudu maso kudu na iya samun mataimakin Shugaban majalisar dattawa - Oshiomhole

An tattaro cewa tsoffin gwamnonin sun yaba da yadda Goje ya gabatar da takararshi, amma suna gann ya kamata ya bi zabin Shugaban kasar.

Tsoffn gwamnonin sun tura wata tawaga zuwa ga Goje domin ya sake duba matsayarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel