Yadda Mata ke kokarin mu'amalan ta da ni - Dangote

Yadda Mata ke kokarin mu'amalan ta da ni - Dangote

Hamshakin dan kasuwar nan dan asalin jihar Kano, Aliko Dangote, shi ne wanda ya fi ko wane bakin mutum tarin dukiya a duniya kuma ya yiwa duk wani bil Adama fintinkau ta fuskar arziki a nahiyyar Afirka kamar yadda Mujallar Forbes ta bayyana.

A yayin wata hirar sa ta Gidauniyar Mo Ibrahim da ya gudanar cikin birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire kwanaki kadan da suka gabata, Dangote ya fayyace ya fayyace labarin wasu ababe da suka shafi rayuwar sa.

Dangote cikin hirar sa ya fadi yadda ya taba karbo Dalar Amurka Biliyan goma daga asusun ajiya na banki kuma ya sanya wannan a kudi gaba ya zuba masu idanu na kurilla domin ya tabbatar da kansa irin cikar sa da batsewa ta fuskar arziki na duniya.

Yadda na ke mu'amala da Mata - Dangote

Yadda na ke mu'amala da Mata - Dangote
Source: Getty Images

Sai dai daga bisani Dangote ya mayar da wannan kudi zuwa asusun sa na ajiya a banki kamar yadda shafin BBC Hausa ya ruwaito. A yayin haka mujallar Forbes ta yi fashin baki na cewar arzikin Dangote ya yi kasa ba kamar yadda ta kasance a baya ba.

Cikin hirar sa da jaridar Legit.ng ta kalato, Dangote ya kuma yi karin haske dangane da yadda mu'amalar sa ta kasance da Mata a sakamakon rashin arziki na aure da ya gaza samu a halin yanzu.

Kasancewar sa attajiri mai mashahuranci irin na sa, Dangote yayin amsa tambayoyi ya yi na'am da cewar Mata da dama na bibiyar sa domin neman samun wurin shiga da walau da manufa ta cin daula da samun nasaba ta dodanar arziki a inda yake ko kuma sabanin haka.

KARANTA KUMA: Tashin Hankali: Ana girbin sassan jikin Fursunonin Musulmi a kasar China

Sai dai mai masaukin baki, Mo Ibrahim, cikin zaurance da ya sanya masu sauraro cikin tuntsura ta dariya ya ce, hamshakan 'yan kasuwa a Najeriya su na da cikakkiyar cancanta ta kasancewa tuzurai.

Yayin tozali da fashin bakin wannan almara, Dangote ya ce a bisa al'ada ta zamantakewa, akwai Mata da dama da ke sha'awar kasancewa tare da shi, sai dai kuwa dole ne wadannan Mata su biyo ta hannun dan uwan sa kuma mashawarci domin tantance su ind ya ke sa ran zai zaba ma sa guda daya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel