Kiwon lafiya: Dalilin da zai sa mata su daina sanya matsattsun wandunan roba - Dr Mbume

Kiwon lafiya: Dalilin da zai sa mata su daina sanya matsattsun wandunan roba - Dr Mbume

- Dr Tony Mbume ya shawarci mata, da su daina sanya matsattsun wanduna (Jeans) da kuma dan kamfai na roba, domin gujewa kamuwa da cutukan farji

- Dr Mbume ya ce kayayyakin da aka sarrafasu daga roba na sanya cutukan farji saboda shigar zafi, wanda ka iya haddasa rikicewar farjin

- Ya kara da cewa ire iren wadannan cutukan na iya haddasa rashin karfin samun kwayayeyn daukar ciki ko kuma lalata mahaifa gaba daya

Wani masanin kwayoyin cuttuka, Dr Tony Mbume ya shawarci mata, da su daina sanya matsattsun wanduna (Jeans), ko 'Leggings', da kuma dan kamfai na roba, domin gujewa kamuwa da cutukan farji.

A cewarsa, da yawan 'yan matan Nigeria na sanya wandunan roba, da suka shafi nau'in 'Jeans', dan kamfai ko 'Leggings' da sunan wasu zasu yi gaye, ba tare da sanin hatsarin da hakan ke da shi ga lafiyar jikinsu ba.

Mbume, wanda ke aiki a babban dakin sarrafa magunguna na CIAGIN, Oke-Afa, Isolo, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Legas cewa kayayyakin da aka sarrafasu daga roba na sanya cutukan farji saboda shigar zafi, wanda ka iya haddasa rikicewar farjin.

KARANTA WANNAN: Assha: Mutane 3 sun mutu, 45 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake a Borno

Kiwon lafiya: Dalilin da zai sa mata su daina sanya matsattsun wandunan roba - Dr Mbume
Kiwon lafiya: Dalilin da zai sa mata su daina sanya matsattsun wandunan roba - Dr Mbume
Asali: Twitter

Ya ce duk wasu kayayyakin da ake sanyawa a kasan wasu kayan da aka hadasu daga nau'in roba, ko leda, na iya adana danshi da gumi, wanda zai iya sanya cuta a farjin mace.

"Wandunan roba kan dumama farjin mace, kuma hakan na iya haddasa konewar wasu kwayoyin halitta, tare da hattasa kaikayi ko warin al'aura, da ma dai sauran cutukan farji.

"Dumin da ake samu idan ana tafiya da matsattsun mandunan roba kan takure fatar jiki, wanda zai iya haddasa cutar bilista," a cewar sa.

Mbume ya ce konewar farjin da kuma kaikayi kan haddasa zubar ruwa mai wari, da ka iya zama babbar cuta ga mace.

Ya kara da cewa ire iren wadannan cutukan na iya zama hatsari ma damar ba a magance su ba, domin hakan na iya haddasa rashin karfin samun kwayayeyn daukar ciki ko kuma lalata mahaifa gaba daya.

Da wannan ne masanin, ya baiwa mata shawara da su rinka sanya wanduna da aka yi su da auduga, domin baiwa farjinsu iska da kuma dakile daukar cutuka, yana mai cewa sanya wandunan da aka sarrafasu daga auduga zai taimakawa farjinsu wajen tsane gumi da kuma baiwa wajen damar shan iska.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel