Ina daya daga cikin shugabannin kasa mafi bakin ciki a duniya

Ina daya daga cikin shugabannin kasa mafi bakin ciki a duniya

Shugaba Muhammadu Buhar ya yi tsokaci kan kashe-kashe da garkuwa da mutane da ya addabi kasar nan kuma ya siffanta kansa matsayin daya daga cikin shugabannin kasa mafi cike da bakin ciki kulli yaumin.

Jihohi irinsu Zamfara, Kaduna da Katsina na fuskantar barazanar yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

A ranar Asabar, wasu masu garkuwa da mutane sun kai zanga-zanga fadar shugaban kasa kan kashe-kashen da ya addabi jihar Zamfara.

A wata jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki, ya bayyana cewa abubuwan da ke faruwa a fadin kasa na matukar damun shugaba Buhari.

KU KARANTA: Kabilar Igbo sun yi murna da nasarar Bala Mohammed a Bauchi

Yace: "Ta yaya zan yi farin ciki da irin kisan gillan da aka yiwa yan uwana. Ni dan Adam ne kuma na fahimci irin bakin cikin da iyalan wadanda abin ya shafa suke ciki na biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa.

"Kawo siyasa cikin kashe-kashen da ke faruwa ya nuna irin jahilcin da ya cika siyasarmu. Kusan kowace mako ina kiran shugabannin tsaro domin samun bayanin abinda akeyi domin kawar da wadannan mugayen irin.

"Na bada umurnin tura dakarun soji dukkan wuraren da yan bindiga ke kai hare-hare kuma mun dukufa wajen ganin cewa mun kawar da wadannan makasan."

Shugaban kasan ya bada tabbacin cewa kawo karshen barandanci ne babban abinda gwamnatinsa ta mayar da hankali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel