Gwamnatin Kano ta tura malamai 11 daga manyan makaratu zuwa kasar Faransa

Gwamnatin Kano ta tura malamai 11 daga manyan makaratu zuwa kasar Faransa

- Jihar Kano ta ce ta dauki nauyin malaman kimiyya 32 da ke koyarwa a manyan makarantun gwamnati na kasar zuwa kasar Faransa domin karo ilimi

- Gwamna Ganduje ya shiga cikin wata yarjejeniya da hukumar kasar Faransa, domin daukar nauyin malaman kimiyya zalla domin karo karatu

- Shirin na gudana ne karkashin ofishin babban mai tallafawa gwamnan ta fuskar manyan makarantu, Dr. Usaini Akilu Jarma

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta dauki nauyin malaman kimiyya 32 da ke koyarwa a manyan makarantun gwamnati na kasar zuwa kasar Faransa domin karo ilimi.

A cikin wata sanarwa daga sakataren watsa labarai na gwamnan jihar, Abba Anwar; ya ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shiga cikin wata yarjejeniya da hukumar kasar Faransa, domin daukar nauyin malaman kimiyya zalla domin karo karatu.

Shirin dai ya fara ne daga shekarar 2016, lokacin da gwamnatin jihar ta aika malamai 11 daga jami'o'in kimiya da fasaha da ke Wudil, Yusuf Maitama Sule da kuma kwalejin koyon sana'o'i ta jihar Kano, domin karatu a bangarori daban daban a jami'o'in kasar Faransa.

KARANTA WANNAN: Moghalu: Mun san an tafka magudi a zaben shugaban kasa, amma ba zamu je kotu ba

Gwamnatin Kano ta tura malamai 11 daga manyan makaratu zuwa kasar Faransa

Gwamnatin Kano ta tura malamai 11 daga manyan makaratu zuwa kasar Faransa
Source: Twitter

A cikin wata wasikar godiya zuwa ga gwamnan jihar, shugaban masu cin gajiyar tallafin zuwa karatu tsakanin kasar Faransa da jihar Kano, Malam Bashir Ado na sashen koyon ilimin 'Chemistry' na kwalejin ilimi ta jihar Kano, ya jinjinawa gwamnan, yana mai nuni da cewa jihar Kano ce mai dalibai mafi yawa a kasar Faransa daga 2016 zuwa yanzu.

Shirin na gudana ne karkashin ofishin babban mai tallafawa gwamnan ta fuskar manyan makarantu, Dr. Usaini Akilu Jarma.

Jihar na biyan dukkanin kudadenta ga kasar Faransa kai tsaye, ba tare da bin ta hannun wani ba, a cewar sanarwar.

A 2017 gwamnatin ta sake tura jerin wasu malamai 11 a zango na biyu, da suka hada da malamai daga kwalejin ilimi ta Sa'adatu Rimi, Kumbutso, kwalejin ilimi ta jihar Kano, kwalejin noma ta Audu Bako da kuma kwalejin kirkira, fasaha da ilimi ta Tudun Wada.

A shekarar 2018, gwamnatin jihar ta dauki nauyin malamai 10 daga manyan makarantun da ke fadin kasar domin karo karatu a kasashen waje.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel