Farashin albasa ya fadi kasa warwas a Katsina

Farashin albasa ya fadi kasa warwas a Katsina

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa farashin albasa ya fadi kasa warwas inda ya fadi daga naira dubu 30,000 a kilo 100 zuwa naira dubu 10,000.

A wani bincike da kamfanin Dillancin Labarai(NAN) tayi a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu ya bayyana cewa a watanni biyu da suka gabata ana siyar da kilo 100 na albasa a kan naira dubu 30,000.

Binciken ya nuna cewa watanni biyu da suka gabata daga jihar Borno ake daukowa inda wasu yan kasuwa ke zuwa daukowa.

A lokacin da aka tuntubi shugaban kungiyar masu siyar da kayan lambu, Alhaji Ahmed Mohammed ya danganta cigaban ga samun albasa a yankin.

Farashin albasa ya fadi kasa warwas a Katsina

Farashin albasa ya fadi kasa warwas a Katsina
Source: UGC

Mohammed ya bayyana cewa manoman karkaran a jihar sun soma girbe albasan su a watan Maris, 2019 wanda suka nome.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta cafke zunzurutun kudi har N54m a filin jirgin sama na Maiduguri

Ya bayyana cewa an samu wadatar albasa wanda yayi sanadiyan faduwar farashi.

Kamfanin Dillancin Labarai ta rahoto cewa albasa ya bazu a kasuwar tumaturi da ke Katsina saboda rashin dadewarsa yayin adana.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa ranar Larabar da ta gabata fittacen attajirin da ya kere kowa tarin dukiya a nahiyyar Afirka kuma shugaban gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana damuwar sa kan yadda talauci ya yiwa al'ummar Arewacin Najeriya katutu.

Dangote yayin bayyana damuwar sa kan wannan kangi da zato sarkakiya a tsakanin al'umma, ya yi kira na neman gwamnonin Arewacin Najeriya da su mike tsaye wurjanjan domin tunkarar lamarin cikin gaggawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel