Ni mashahurin tauraro ne tun kafin zuwan Facebook da Tuwita - Adam Zango

Ni mashahurin tauraro ne tun kafin zuwan Facebook da Tuwita - Adam Zango

Abinda Shahrarren mawaki kuma jarumin fina-finan Kannywood, Adam A. Zango ya yi na jinjinawa kansa a matsayin bahaushen da ya fi yin fice cikin hausawan duniya ya bar baya da kura, yayinda jama'a suka dinga caccakansa.

A wata faifan bidiyo da ya wallafa a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa ta Instagram ya ce "Ni ne Bahaushen da na fi ko wane Bahaushe suna da masoya a duniya."

Adam Zango ya bayyana cewa ba shi ya gamo haka ba, masu bincike ne suka binciko hakan kuma ya samu labari.

KU KARANTA: Ta bayyana: NJC ta bukaci Buhari ya yiwa tsohon CJN Walter Onnoghen ritayar dole

Amma jama'ar kasar Hausa sun nuna rashin jin dadinsu da irin wadannan kalamai da Adam Zango yayi inda suka kwantatashi da wasu mashahuran Hausawa wadanda aka san su a fadin duniya irinsu malamai (Sheik Kabiru Gombe da Isa Fantami), Yan kasuwa (Dangote), Sarakuna (Sarkin Kano), da shugabanni (Buhari).

Akan hakan kuma, sai da Adam Zango ya sake martani inda yace hadashi da irin wadannan mutane nasarace gareshi.

Yace: "Hadani da wadanan manyan mutanen kadai nasarace! DON NACE NAFI KO WANI BAHAUSHE SUNA A DUNIYA. Toh ai ba yi na bane, daga ALLAH ne. idan kuma akwai wanda zai iya hana ruwa gudu ai sai ya gwada.

Duk wanda yake musu ya fara bincike a cikin danginsu (family) ko a wani kasa (country) suke zai sami kyakykyawar amsa. A daina yaudararku da social media followers, coz no be today we start am now. AI ZANGO SUPER STAR NE TUN KAFIN ZUWAN FACEBOOK TALK LESS OF INSTAGRAM!

Kuma na fada muku page dina na masoyana ne ba makiyana ba, idan rubutu na yana baka haushi sai kayi unfollowing dina tunda ba dole bane. Ni na san cewa masoyina ko me nayi matukar bai sabawa addini na ba ba zai gujeni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel