Tonon asiri: Mun rantse da Allah Adeleke bai zana jarabawar WAEC ba - Shaidu

Tonon asiri: Mun rantse da Allah Adeleke bai zana jarabawar WAEC ba - Shaidu

Wasu shaidu guda biyu da aka gabatar akan shari'ar Sanata Ademola Adeleke da ake zarginsa da aikata laifuka bakwai da suka shafi satar jarabawa, a ranar Laraba sun shaidawa babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja cewar ba su ga Sanatan a dakin zana jarabawar ba.

Shaidun, Mr Emmanuel Adesola da kuma Enoch Adigun, wadanda gaba dayansu malamai ne, a yayin da jami'i mai shigar da kara Mr Simon Lough ya gabatar da su a gaban kotun, sun bayyana cewa su ne suka sa ido yayin zana jarabawar WAEC a makarantar sakandire ta Ojo -Aro Community Grammar da ke jihar Osun State a shekar 2017.

Adesola ya shaidawa kotun cewa a lokacin da ya je makarantar, ya bukaci a bashi sunayen daliban da zasu zana jarabawar gaba daya, amma aka ce ba a kammala hadawa ba.

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: Buhari, Osinbajo, SGF, ministoci 20 sun shiga taron majalisar zartaswa

Tonon asiri: Mun rantse da Allah Adeleke bai zana jarabawar WAEC ba - Shaidu

Tonon asiri: Mun rantse da Allah Adeleke bai zana jarabawar WAEC ba - Shaidu
Source: Depositphotos

"Banga Sanata Adeleke a cikin dakin zana jarabawar ba, shi sanannen mutum ne, na tabbata da na ganshi idan da har ya zana jarabawar," a cewar shaidar.

A na shi bangaren, Adigun ya shaidawa kotun cewa ya ga daya daga cikin wadanda ake zargi, Sikiru Adeleke a dakin zana jarabawar, yana mai cewa yayi mamakin ganinsa kasancewar shi ne mafi girma daga cikin daliban amma bai ga Sanata Adeleke ba.

Mai shari'ar, Inyang Ekwo ya dage zaman kotun kan shari'ar har sai ranar 10 da 11 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron karar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel