Najeriya na cikin kasashen da ke fama da matsananciyar yunwa – Majalisar dinkin duniya

Najeriya na cikin kasashen da ke fama da matsananciyar yunwa – Majalisar dinkin duniya

Rahotanni daga majalisar dinkin duniya da Ingila ya nuna cewa sama da mutane miliyan 113 a fadin kasashe 53 ne suka fuskanci matsananciyar yunwa a shekarar da ya gabata tare da rikici, annobar sauyin yanayi da kuma matsalolin tattalin arziki wanda ke haddasa rikicin abinci.

Kungiyar abinci da harkar noma, shirin abinci na duniya (WFP) da kungiyar da ke kawo rahoton duniya kan rikicin abinci na 2019, ya nuna cewa cikin shekaru uku da suka gabata ana ci gaba da samun karin mutane da abun ke shafa

Rahoton ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 113 a fadin kasashe 53 da suka fuskanci yunwa na bukatar tallafin gaggawa na abinci masu gina jiki da sauran kayan masarufi.

Kasashen da suka fuskanci matsanancin yunwa a 2018 sun hada da Yemen, kasar Congo, Afghanistan, Ethiopia, Syria, Sudan, Kudancin Sudan da kuma arewacin Najeriya. Wadannan kasashe takwas sun eke da kaso biyu cikin uku na mutanen da suka fuskanci matsanancin yunwa, inda hakan ya kai kimanin mutane miliyan 72.

Najeriya na cikin kasashen da ke fama da matsananciyar yunwa – Majalisar dinkin duniya
Najeriya na cikin kasashen da ke fama da matsananciyar yunwa – Majalisar dinkin duniya
Asali: UGC

An tattaro cewa koda dai akwai akalla mutane miliyan 11 da ake ganin sun fuskanci matsalar abinci a 2018 idan aka kwatanta da na 2017, a kasashe 17, matsananin yunwa na nan yadda yake ko kuma ya karu.

KU KARANTA KUMA: Zababbun mambobi 40 na majalisan dokokin Lagas za su karbi takardun shaidar cin zabe a ranar Juma’a - INEC

Har ila yau, akwai wasu karin mutane miliyan 143 a wasu kasashe 42 da ke gab da fadawa matsananciyar yunwa. Wadannan mutane na fuskantar barazanar fadawa a rikici ko kuma mafi munin haka idan suka fada halin fargaba, cewar rahoton.

Annobar sauyin yanayi ya jefa wasu mutane miliyan 29 zuwa matsanancciyar rashin tsaro na abinci a 2018, inji rahoton, sannan kuma cewa adadin ya ware kasashe 13, ciki harda Koriya ta arewa da Venezuela saboda tazarar kididdiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel