Da duminsa: Buhari ya isa kasar Senegal (Hotuna)
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Dakar, babar birnin kasar Senegal da daren Litinin, 2 ga watan Afrilu, 2019 inda aka gayyacesa a matsayin babban bako na musamman a bikin rantsar da shugaban kasar Senegal, Macky Sall.
Mun kawo muku rahoton cewa tafiyarsa na farko bayan nasara a zaben shugaban kasa, Shugaba Muhammadu Buhari zai garzaya kasar Senegal domin amsa goron gayyatar shugaban kasar, Macky Sall, wanda za'a rantsar a zangoo na biyu ranan Talata, 2 ga watan Afrilu,2019.

Asali: Facebook
Legit.ng ta samu wannan rahoton daga fadar shugaban kasa da safiyar Litinin, 1 ga watan Afrilu inda ta ce:
"Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja yau domin zuwa Dakar, birnin Senegal domin halartan bikin rantsar da shugaban kasar Senegal Macky Sall, bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa karo na biu.
"Domin amsa goron gayyatar shugaban kasan, shugaba Buhari wanda shine shugaba kungiyar ECOWAS zai zama babban bako tare da sauran shugabannin nahiyar Afrika a cibiyar Diamniadio ranar Talata."
Shugaban kasa zai tafi tare sa gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar; gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i; da gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko AlMakura."
Sauran sune ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; mai shawarar tsaron kasa, Babagana Munguno; shugaban hukumar NIA, Amb ahmed Rufa'i da sauransu.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng