Yanzu yanzu: Mohammed Dantani, dan majalisar tarayya ya rasu a Abuja

Yanzu yanzu: Mohammed Dantani, dan majalisar tarayya ya rasu a Abuja

Kakakin majalisar wakilan tarayya Mr Yakubu Dogara, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar dan majalisa mai wakiltar mazabar Yauri/Shangi/Ngaski a majalisar wakilan tarayya da ke a jihar Lebbi, Hon. Mohammed Dantani.

A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Juma'a, Dogara ya ce ya samu labarin rasuwar dan majalisar a Abuja bayan doguwar jinya da ya sha, yana mai cewa mutuwar ta girgiza shi matuka.

Kakakin majalisar ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya, wanda kuma ke bayar da gagarumar gudunmowa a majalisar wakilan tarayya a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi da kuma mamba a majalisar tarayyar.

KARANTA WANNAN: Maganar boye ta fito fili: An gano dalilin da yasa Ganduje ya kada Abba a Kano

Yanzu yanzu: Mohammed Dantani, dan majalisar tarayya ya rasu a Abuja
Yanzu yanzu: Mohammed Dantani, dan majalisar tarayya ya rasu a Abuja
Asali: UGC

"A matsayinsa na dan majalisa kuma mai yiwa jama'a aiki, marigayi Dantani ya taimakawa rayuwar jama'a da dama ta hanyar gudunmowarsa a majalisar tarayya, ayyukan bunkasa mazabarsa da kuma taimakawa gajiyayyu a cikin al'umma.

"Hakika majalisar ta rasa mutum mai son zaman lafiya, wanda ke da nagarta kuma ya kwashe kusan rayuwarsa wajen yiwa demokaraddiyya hidima.

"A madadin shuwagabanni da kafatanin mambobin majalisar wakilan tarayya, ina mika sakon ta'aziyyata ga iyalan mamacin, mazabarsa, gwamnati da kuma al'ummar jihar Kebbi bisa ga wannan babban rashi.

"Allah ya jikansa da rahama," a cewar Dogara.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel