Da dumi-dumi: Atiku ya yi martani yayinda Fintiri ya lashe zaben gwamnan Adamawa

Da dumi-dumi: Atiku ya yi martani yayinda Fintiri ya lashe zaben gwamnan Adamawa

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi martani akan nasarar jam’iyyar a zaben gwamna da aka yi a jihar Adamawa, wacce ta kasance mahaifarsa.

Atiku, wanda ya yaba ma mutanen jihar akan zabar dan takarar gwamna na PDP, Ahmadu Fintiri, yace yana zuba ido nan gaba don aiki tare da zababben gwamnan.

“Ina taya murna ga mutumin mutanenmu, zababben gwamna, Ahmadu Fintiri.

“Burin da mutanenmu na Adamawa suka daura a kanka yayi daidai sannan ina duba ga aiki tare da kai anan gaba domin sake mayar da jiharmu ga tafarkin inganci,” inji shi.

KU KARANTA KUMA:

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, zababben gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Fintiri, ya yi alkawarin biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000 idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi.

Fintiri wanda ya yi nasarar lashe zaben gwamna a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya dauki wannan alkawarin ne a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris yayinda yake zantawa da manema labarai a Yola.

Ya kayar da gwamnan jihar mai ci a yanzu, Mohammadu Bindow na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da kuma sauran yan takara 28 a zaben da aka kammala kwanan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel