Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000

Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000

Zababben gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Fintiri, ya yi alkawarin biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000 idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi.

Fintiri wanda ya yi nasarar lashe zaben gwamna a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya dauki wannan alkawarin ne a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris yayinda yake zantawa da manema labarai a Yola.

Ya kayar da gwamnan jihar mai ci a yanzu, Mohammadu Bindow na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da kuma sauran yan takara 28 a zaben da aka kammala kwanan nan.

Ya bayyana cewa: “Zan ba ma’aikatar gwamnati kulawa na mussamman sannan zan kara inganta ta.

“Domin tabbatar da muhimmancin haka, ni zan fara aiwatar da shi, domin kada mu fuskanci yajin aikin ma’aikata,” inji Fintiri.

Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000
Zababben gwamnan Adamawa ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashi N30,000
Asali: UGC

Ya kuma baiwa dalibai tabbacin cewa gwamnatinsa za ta jajirce wajen sabonta shirin daukar nauyin karatunsu, samar da shirin tallafi ga matasa da sauran shirye-shiryen da zai kawo ci gaba a jihar.

Ya mika godiya ga mutanen jihar kan zabarsa da suka yi sannan yayi alkawarin cewa ba zai taba basu kunya ba.

KU KARANTA KUMA: Majalisar malamai sun bayyana zaben Kano a matsayin fashin damokradiyya

“Mutane sun bamu kuri’unsu kuma Allah ya tabbatar da hakan a yau.

“Za mu tabbatar ganin cewa mun isar da alkawaran zaben da muka dauka.

“Muna bukatar mutane da su kwantar da hankalinsu, sannan ku zamo masu bin doka yayinda kuke murna da jiran bikin rantsar da mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel