Zaben Sokoto: APC ta samu kujeru 16 yayin da PDP ta samu 14 a majalisar dokoki
Sakamakon zaben 2019 zuwa ga kujeru 30 na majalisar dokokin jihar Sokoto ya bayyana cewa a majalisar dokokin jihar ta 9, jam'iyyar APC ta samu kujeru 16 yayin da jam'iyyar PDP ta samu kujeru 14.
Ga mambobin majalisar ta 8 a jihar Sokoto, akwai mambobi 19 na PDP, wadanda 10 daga cikinsu suka fadi zaben 2019, yayin da guda daya bai ma tsaya takara ba.
Mamban da bai tsaya takarar kujerar majalisar dokokin jihar ba shi ne kakakin majalisar, Salihu Maidaji wanda ke wakiltar mazabar Gada ta Gabas.
KARANTA WANNAN: Rahoto na musamman: Adadin kudaden da PENCOM ta tara ya kai Naira tiriliyan 8.67
A mai makon hakan, ya tsaya takarar kujerar sanatan mazabar Sokoto ta Gabas amma ya sha kasa a hannun sanatan mazabar mai ci Ibrahim Gobir na jam'iyyar APC.
Ga sunayen 'yan majalisun dokokin da mazabunsu tare da jam'iyyunsu:
1) Aminu Magaji APC- Dange/Shuni
2) Mustapha Abdullahi APC- Sokoto South 1
3)Malami Ahmed PDP- Sokoto South II
4) Suke Romo PDP- Tambuwal West
5) Mode Ladan PDP Tambuwal East
6)Musa Miko PDP- Tangaza
7) Murtala Maigona APC- Wamakko
8) Aminu Achida APC-Wurno
9) Shehu Yabo APC- Yabo
10) Haliru Buhari PDP- Sokoto North 1
11) Ibrahim Arzika PDP- Sokoto North II
12) Abdullahi Randa PDP- Tureta
13) Umaru Sahabi PDP- Binji
14) Abubakar Magaji PDP- Bodinga North
15) Bala Tukur APC- Bodinga South
16) Altine Kyadawa APC- Gada West
17) Kabiru Dauda APC- Bada East
18) Mustapha Balle PDP- Gudu
19) Bello Idris APC- Gwadabawa South
20) Abdullahi Garba APC- Gwadabawa North
21) Bello Ambarura APC- Illela
22) Habibu Modachi PDP- Isa
23) Abdullahi Mahmud PDP- Kware
24) Abdullahi Zakari APC- Rabah
25) Almustapha Aminu PDP- Sabon Birni North
26) Saidu Ibrahim APC- Sabon Birni South
27) Alhaji Maidawa APC- Shagari
28) Atiku Liman PDP- Silame
29) Isa Harisu APC- Kebbe
30) Faruku Amadu APC- Goronyo
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng