Mataimakin gwamnan Kano da wasu kwamishanoni suka shirya ta'addancin zaben Kano - Shugaban PDP

Mataimakin gwamnan Kano da wasu kwamishanoni suka shirya ta'addancin zaben Kano - Shugaban PDP

Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Kano, Rabiu Bichi, ya ce da alamun bangan siyasa karkashin gwamnatin All Progressives Congress (APC), abin alfahari ne.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya lashe zaben gwamnan jihar inda ya lallasa Abba Kabir Yusuf, na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP a zagayen zabe na biyu da ya gudana ranar 23 ga watan Maris, 2019.

Yayinda yake magana da manema labarai a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, Bichi ya yi watsi da jawabin kungiyar kare muradun Buhari BMO cewa PDP ce ta jagoranci bangar siyasa a jihar.

Bichi yace abin takaici ne ace kungiyar ta goyi bayan Ganduje da abokan sharrinsa wadanda suka dauki nauyin yan daba da magudin zaben jihar.

KU KARANTA: Tinubu ko Osinbajp APC zata tsayar takaran shugaban kasa a 2023 - Tanko Yakassai

Yace: "Da irin wannan magana, BMO da iyayen gidansu sun nuna cewa rikice-rikicen abin alfahari ne karkashin gwamnatin APC tunda wadanda sukayi wannan abu na samu kyawawan kyaututtuja daga INEC kamar yadda muka gani a Kano."

"APC ta amfana da ta'addancin zabe da mataimakin gwamna da wasu kwamishanoni suka shirya."

"Muna jaddada cewa wakilanmu na da hujjoji, masu lura da zabe da mutan Kano sun san yadda APC ta dauki nauyin yan daba domin cin mutuncin mabiyanmu da kuma hana magoya bayanmu zabe domin kawai Ganduje ya cigaba da mulki."

"Duniya ta gani cewa mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna, da kwamishnan kananan hukumomi, Alhaji Sule Garo, sun shiga hannun yan sanda kan laifin hargitsa zaben karamar hukumar Gama bayan Ganduje ya gano cewa zai fadi."

"Abinda ya faru a Gama dake karamar hukumar Nasarawa inda akayi saye-sayen kuri'u, barazana ga mutane, zaben karya, kamar yadda aka shaida a dukkan sauran kananan hukumomi ya nuna cewa Ganduje munafiki ne."

Bichi ya ce jam'iyyar PDP za ta kwato hakkinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel