Kwanaki 13 hannun masu garkuwa da mutane: Abin ba dadi amma na godewa Allah - Alaramma Ahmed Suleiman

Kwanaki 13 hannun masu garkuwa da mutane: Abin ba dadi amma na godewa Allah - Alaramma Ahmed Suleiman

Babban malamin addinin Islama Sheik Ahmad Suleiman a ranar Laraba ya bayyana cewa abubuwan da idonsa ya gani a hannun masu garkuwa da mutane, ya fi karfin fadin baki.

Yayinda yake jawabi a fadar mai martaba sarkin Katsina, inda manema labarai suka halarta, Malam Ahmad Suleiman ya ce " ba abun dadi bane mutum ya tsaya hannun masu garkuwa da mutane na sama da kwanaki 10."

"Abin ba dadi amma na godewa Allah tunda na tsira yanzu. Kullun abinda suke fada mana shine tunda hukumar ta shiga yanzu, Malam ba zaku goma gida ba, ko an kawo kudin nan sai mun kasheku."

"Kullum babu abinda mukeji a kunnuwanmu sai za'a kashemu. Kuma za'a zo gabanmu a dinga harba bindiga muna ji. Gaskiyar magana wadannan kwanaki masu wahala ne sosai amma mun gode Allah. Sai dai a ciki akwai karatu sosai, karatu mai amfani."

"Haka yaran nan za su taru su dinga rusa kuka. Wani lokaci suyi kukan, suyi ina basu hakuri, wani lokacin kuma nine zan yi kukan suna lallashi na. Za'a zo da daddare a kofar dakin da ba za ka iya shiga ba sai ka sunkuya, sai ka durkusa da gwiwa za ka shiga dakin nan, sannan a kwantar da bindigogi ayi saitinsu cikin daki."

"Sannan suyi ta shan wiwi suna buso mana hayaki cikin daki. Ba ma iya bacci daddare, da rana ga barazana. Wani lokaci sai su barmu da yunwa su hanamu abinci, su hanamu ruwa, dukkan wadannan abin muka gani. Ubangiji muke roka idan laifi mukayi ya yafe mana."

"Ina godewa Sojin Najeriya musamman babban hafsan sojin, Janar Tukur Buratai, ina godewa Malamanmu da suke kai komo, suna fadi suna tashi musamman kan ganin cewa kudinnan da aka nema, daga karshe kuma Allah ya fitar damu ba tare da komai ba."

KU KARANTA: Mutane miliyan 25.6 suka nemi aikin NNPC

Mun kawo rahoton cewa an ceto malamain tare da dalibansa a daren Talata, 26 ga watan Maris misalan karfe 12 na dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel