'Yan Najeriya sun sayi katin wayar salula na N767.23bn cikin watanni uku - NCC

'Yan Najeriya sun sayi katin wayar salula na N767.23bn cikin watanni uku - NCC

Wani sabon bincike da aka gudanar ya bayyana yadda al'ummar Najeriya masu amfani da wayoyin salula suka kashe Naira biliyan 767.23 wajen sayan katin waya a tsakanin watan Nuwamban 2018 zuwa Janairun 2019.

Domin gudanar da harkokin sadarwa na aika sakonni, kiran waya da kuma shiga yanar gizo, al'ummar Najeriya sun kashe kimanin Naira Biliyan 767.23 a tsakanin watan Nuwamban 2018 zuwa Janairun 2019 wajen sayan katin waya kamar yadda wani sabon bincike ya bayyana.

'Yan Najeriya sun sayi katin wayar salula na N767.23bn cikin watanni uku - NCC
'Yan Najeriya sun sayi katin wayar salula na N767.23bn cikin watanni uku - NCC
Asali: Twitter

Kamfanin sadarwa na Najeriya NCC, Nigerian Communication Commission, shi ne ya gudanar da wannan bincike kan adadin al'ummar Najeriya masu mallakin layin waya mai rajista wajen amfani a wayoyin su sadarwa cikin watanni uku.

A watan Nuwamban 2018, binciken NCC ya bayyana yadda masu sayen katin waya domin shiga yanar gizo watau sayen Data suka kashe Naira miliyan 168.73 a layukan sadarwa na MTN, GLO, Airtel, da kuma 9Mobile.

A watan Dasumba kuma, al'ummar Najeriya sun batar da Naira Miliyan 172.63 wajen sayen Data yayin da adadi na masu mallakin layi na wayoyin sadarwa ya kai Miliyan 173.63 a watan Janairu na shekarar da muke ciki.

KARANTA KUMA: Ta'addanci da sayen kuri'u sun dabaibaye zaben cike gibi na gwamnan jihar Kano - EU

Yayin da sayen katin waya ya kasance kashin baya na samun kudaden shiga ga dukkanin kamfanonin sadarwar kasar nan, al'ummar Najeriya sun batar da Naira Biliyan 258.74 wajen sayen kati a watan Janairu na bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel