Dan takarar gwamnan Yobe a PDP ya ce ba zai kalubalanci nasarar APC a kotu ba

Dan takarar gwamnan Yobe a PDP ya ce ba zai kalubalanci nasarar APC a kotu ba

- Dan takarar gwamnan jihar Yobe karkashin jam'iyyar PDP, ya ce ba zai kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar a kotun sauraron korafe korafen zabe ba

- Mr Iliya, dan takarar jam'iyyar ta PDP, ya ce ya amince da nasarar Mai Mala Buni na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar na gaba

- Ya bukaci zababben gwamnan jihar da ya yi amfani da wannan kujerar ta sa wajen kyautatawa al'ummar jihar ba tare da ya duba banbancin siyasa ba

Dan takarar gwamnan jihar Yobe karkashin jam'iyyar PDP, Iliya Damagum, a ranar Talata, ya ce ba zai kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar a kotun sauraron korafe korafen zabe na jihar ba.

Mr Iliya ya shaidawa manema labarai a Damagum bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP wacce ta yi nazari kan sakamakon zaben gwamnan jihar, cewar ya amince da nasarar Mai Mala Buni na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar na gaba.

"Ba a rasa bangarorin da aka karya dokokin zabe ba, amma dai an sanar da wanda ya lashe zabe. Ba mu da wani zabi da ya wuce mu amince da sakamakon zaben tunda dsi hakan Allah ya kaddara," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: Daga INEC: Sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi zagaye na biyu

Mai Mala Buni: Zababben gwamnan jihar Yobe
Mai Mala Buni: Zababben gwamnan jihar Yobe
Asali: Original

Mr Iliya ya ce tuni ya taya zababben gwamnan murnar wannan nasarar da ya samu.

"Tuni na taya Mai Mala zababben gwamnan jihar murna, na kuma na yi kira a gare shi da ya kalli Yobe a matsayin mazabarsa, tunda dai yanzu Allah ya ba shi damar yin hakan," a cewar sa.

Ya bukaci zababben gwamnan jihar da ya yi amfani da wannan kujerar ta sa wajen kyautatawa al'ummar jihar ba tare da ya duba banbancin siyasa ba.

Mr Iliya ya jinjinawa magoya bayansa da kuma 'yan siyasar jihar bisa yadda suka nuna dattako yayin da aka gudanar da zaben da ma bayan kammala shi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel