Sanata Aliyu Wamako, dan takara Ahmed Aliyu sun taya Tambuwal murna

Sanata Aliyu Wamako, dan takara Ahmed Aliyu sun taya Tambuwal murna

Dan takaran gwamna jihar Sokoto karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Ahmed Aliyu, da Sanata Aliyu Wamakko, sun kira gwamna Aminu Tambuwal na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP domin tayasa murnar nasarar zabe.

Shafin Tuwitan gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana hakan ne bayan hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zama kanta watau INEC ta alanta gwamna Aminu Tambuwal matsayin wanda ya lashe zaben.

Ya kada Ahmed Aliyu da tazarar kuri'u 342.

KU KARANTA: An damke ma'aikatan asibiti 2 kan sayar da jariri

Aliyu ya kasance matimakin gwamnan jihar Sokoto amma yayi murabus sakamakon fitar Tambuwal daga APC zuwa PDP, saboda niyyarsa na takaran kujeran shugaban kasa. Sai ya tsaya takarar gwamna.

Wamakko, magabacin Tambuwal, ne wanda ya taimaka masa wajen zama gwamnan jihar a shekarar 2015.

Gwamna Aminu Tambuwal na PDP yana da kuri’u 489,558 yayin da ‘Dan takarar APC Aliyu Ahmed ya samu kuri’a 486,145 a sakamakon da aka fitar a karon farko. A wancan lokaci Tambuwal ya bada ratar kuri'a 3, 413.

A zaben na cike-gibi da aka yi ranar Asabar, APC ta samu kuri’u 18, 342, inda jam’iyyar PDP mai rike da jihar ta ke baya da kuri’a 16, 987. Hakan na nufin jam’iyyar APC ta ba gwamna Tambuwal tazarar kuri’a 1, 355.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel