Ganduje ya ce zaben Kano Demokradiyya ce zalla, wadanda basu ji dadi ba suyi hakuri

Ganduje ya ce zaben Kano Demokradiyya ce zalla, wadanda basu ji dadi ba suyi hakuri

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya siffanta zaben jihar Kano a matsayin demokradiyya zalla.

Ya godewa dukkan magoya bayansa kan fitowa kwansu da kwarkwatansu domin zabensa. Hakazalika yayi kira ga wadanda basu ji dadin sakamakon ba su yi hakuri.

Yace: "Muna roko a kasance cikin zaman lafiya. Masu murna suyi murna cikin lumana domin gujewa barazana kuma wadanda basu ji dadi ba suyi hakuri."

"Amma abinda zan iya cewa shine wannan demokradiyya ce kuma muna bukatan juna. Na yi imanin cewa zamu kawo cigaba jihar Kano dubi ga irin ayyukan da mukayi."

"Ko shakka babu, idan ka samu nasara a zango na biyu, za kayi ne domin cigaban abubuwan da ka fara saboda kawowa jiha cigaba. Muna kira ga abokan hamayyarmu da mukayi takara tare su zo mu hada kai domin cigaban Kano."

KU KARANTA: Ganduje, Tambuwal, Lalong, Ortom sun yi tazarce

An alanta Ganduje matsayin zakaran zabe a ranar Lahadi bayan ya samu jimillar kuri'u 1,033,695 inda ya zarcewa mai biye da shi, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP, wanda ya samu kuri'u 1,024,713.

Abba Kabir ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta PDP bata amince da wannan sakamakon ba kuma zasu garzaya kotu domin kwato hakkinsu.

Yace: "Sakamakon zaben jihar Kano da INEC ta sanar da yammacin nan (Asabar) bamu amince da shi ba. Zamu hadu a kotu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel