Karshen duniya: An jefar da jariri da wasika mai sosa zuciya a garin Kaduna

Karshen duniya: An jefar da jariri da wasika mai sosa zuciya a garin Kaduna

Wani lamari da ya tayar da hankalin al'umma da dama da kuma ya auku a ranar Alhamis din da ta gabata shine na wani jariri da aka tsinta da misalin karfe 11 na dare a unguwar da ke bayan Asibitin Badarawa, jihar Kaduna.

A tattare da jaririn ko jaririyar anjefar da ita da wata wasika mai dauke d nuna nadamar yarinyar na aikata wannan mummunar dabi'ar wacce tace yafaru ne ba dason zuciyar ta ba, kuma ta jefar da jaririn ne sabo da tana gudun halin da iyayen ta zasu shiga dalilin wannan aika-aikan da tayi bayan da kyakkyawar tarbiyar da iyayenta suka bata.

Karshen duniya: An jefar da jariri da wasika mai sosa zuciya a garin Kaduna
Karshen duniya: An jefar da jariri da wasika mai sosa zuciya a garin Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA: An gargadi Buhari kan kara haraji

Haka nan ma kuma ita mahaifiyar jaririn ta roki yan'uwa da suyi mata addu'ar samun gafara da yafiya wajen Allah.

A cikin Hoton Zakuga Yanda wasu mata suka rike jaririn tare da uban kasa uban al'umma Hakimin Gundumar Kawo Alhaji Jibreel m. Magaji.

Ya Allah ka shirya mana zuria.

Ga dai hotunan jaririn nan a kasa da hakimin garin da ma kuma wasikar da aka jefar da jaririn da ita:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel