Shugabancin majalisar tarayya ta 9: Zababbun sanatocin APC sun gargadi jam'iyyar

Shugabancin majalisar tarayya ta 9: Zababbun sanatocin APC sun gargadi jam'iyyar

- Zababbun sanatocin APC sun yi gargadin cewa idan aka bada shugabancin majalisar dattijai ga wasu tsirarun mutane zai haddasa babban rikici a jam'iyyar

- Sanatocin APC sun kuma yi zargin cewa jam'iyyar PDP na kulla makarkashiya kan wanda zai zama shugaban majalisar dattijan kamar yadda suka yi a 2015

- A majalisar dattijai, Ahmed Lawan, Danjuma Goje, Ali Ndume da Abdullahi Adamu su ne aka fi kallo a matsayin wadanda suka cancanta da shugabancin majalisar

Zababbun sanatoci karkashin jam'iyyar APC sun yi gargadin cewa idan har aka kuskura aka bada shugabancin majalisar dattijai ga wasu tsirarun mutane, to kuwa hakan zai haddasa babban rikici a cikin jam'iyyar.

A ranar Juma'a, Legit.ng ta ruwaito maku cewa an fara kulla makarkashiya tare da zawarcin shugabancin majalisar tarayya ta 9.

A majalisar dattijai, Ahmed Lawan (Yobe), Danjuma Goje (Gombe), Ali Ndume (Borno) da Abdullahi Adamu (Nasarawa) su ne aka fi kallo a matsayin wadanda suka cancanta da shugabancin majalisar.

KARANTA WANNAN: Arewa za ta gabatar da dan takarar shugaban kasa da yafi cancanta a 2023 - Shettima

Shugabancin majalisar tarayya ta 9: Zababbun sanatocin APC sun gargadi jam'iyyar
Shugabancin majalisar tarayya ta 9: Zababbun sanatocin APC sun gargadi jam'iyyar
Asali: UGC

Sai dai, wani babban zababben sanata, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya yi gargadi cewa idan har aka raba shugabancin majalisar ga wasu tsirarun mutane kawai, to kuwa zai haddasa rikicin da zai yi wuyar magancewa a jam'iyyar.

A cewarsa, jam'iyyar PDP na kulla makarkashiya kan wanda zai zama shugaban majalisar dattijan kamar yadda suka yi a 2015.

"Idan har suka aikata hakan, to zai haddasa rikici kuma ba zai taimakawa jam'iyyar ba a karshen karshe. Ya kamata a raba shugabancin majalisar ga tsarin shiyya shiyya kawai, ba wai ga wasu tsirarun mutane ba."

Wani sanatan wanda shima ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana cewa raba mukamin shugabancin majalisar zai kawo rabuwar kawuna a cikin majalisar.

Ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbata an raba shugabancin majalisar a tsarin shiyya shiyya kamar yadda aka gudanarwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel