In-kunne-yaji: An gargadi gwamnatin tarayya kan kudirin ta na kara haraji

In-kunne-yaji: An gargadi gwamnatin tarayya kan kudirin ta na kara haraji

Kungiyar masu kamfanonin kere-kere da ababen masarrufi watau Manufacturers Association of Nigeria (MAN) a ranar Alhamis ta gargadi gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari akan kudurin ta na kara harajin samar da kayayyaki na VAT.

Shugaban kungiyar a mataki na kasa, Mista Segun Ajayi Kadir shine ya bayar da wannan gargadin lokacin da yake mayar da martani akan kudurin na gwamnati da hukumar tattara haraji ta kasa watau Federal Inland Revenue Service (FIRS) take shirin dabbakawa a shekarar 2019.

In-kunne-yaji: An gargadi gwamnatin tarayya kan kudirin ta na kara haraji
In-kunne-yaji: An gargadi gwamnatin tarayya kan kudirin ta na kara haraji
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta rufe kes din tsohon Alkalin alkalai

A cewar sa, ko kusa wannan kudurin na gwamnatin ba zai yi wa su masu sana'ar ta samar da abubuwan ba da ma kananun 'yan tireda dake hada-hadar siyar da su har zuwa talakawan dake anfani da kayayyakin na masarufi ba.

Haka zalika daga karshe sai ya yi kira ga gwamnatin da ta dubi duminiyar 'yan kasar ta hanyar janye wannnan kudurin na ta domin maslahar kowa da kowa.

A baya dai mun kawo maku labarin cewa, Hukumar gwamnatin tarayyar Najeriya dake da alhakin tattara haraji ta kasa watau Federal Inland Revenue Service (FIRS) a ranar Talata ta bukaci 'yan Najeriya da su kwana da shirin ko-ta-kwana na karin harin kayayyaki a shekarar nan ta 2019.

Hukumar ta FIRS ta bayyana cewa tana nan tana shirye-shiryen yin karin harajin na bangaren da ake kira da Value Added Tax (VAT) da kaso 35 zuwa 50 cikin dari domin samar da kudaden shigar da za a iya dabbaka kasafin kudin na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel