Assha: Dan daba ya kashe wanda ake zargi da kashe wata mata tare da kona gawarsa
- Wani dan daba ya kashe tare da kona wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne da aka kama shi da laifin yin filla-fila da naman jikin wata mata da ya kashe
- Wata majiya ta ce mutumin ya kasance yana yin abubuwa kamar na mai tabin hankali da rana amma yana kashe mutane da daddare, musamman ma mata
- Rahotanni sun bayyana cewa mata ukku sun rasa rayukansu a irin wannan yanayin a cikin watan da ya gabata
Rahotanni sun bayyana cewa wani dan daba a garin Akenpai, Yenogoa, babban birnin jihar Bayelsa, ya kashe tare da kona wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne da aka kama shi da laifin yin filla-fila da naman jikin wata mata da ya kashe.
An cafke shi ne a lokacin da ya ke kokarin fede cikin matar da ya kashe ta, da aka bayyana sunanta da 'Best', 'yar asalin garin Epie.
Ganau sun bayyana cewa dan dabar ya dauki hukunci a hannunsa na kashe matsafin bayan da ya rinka waina gatarin da ke hannunsa wanda ya kashe matar da shi.
KARANTA WANNAN: Yawan cin kifi zai iya magance kamuwa da cutar asma - Bnciken masana

Asali: Depositphotos
Wata majiya daga al'ummar garin ta ce mutumin wanda suma kansu jama'ar garin basu sanshi ba ya kasance yana yin abubuwa kamar na mai tabin hankali da rana amma yana kashe mutane da daddare, musamman ma mata.
Rahotanni sun bayyana cewa mata ukku sun rasa rayukansu a irin wannan yanayin a cikin watan da ya gabata.
Rundunar 'yan sanda ta bakin mai magana da yawunta, DSP Asinim Butswat, ta ce da wanda ake zargi yana kisan da kuma matan da aka yi zargin ya kashe, duk ana zargin suna da tabin hankali.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng